‘Yan Jarida Ku Karfafa Dorewar Zaman Lafiya A Nijeriya – Gwamna Masari

- Advertisement -

‘Yan Jarida Ku Karfafa Dorewar Zaman Lafiya A Nijeriya – Gwamna Masari

Daga Sagir Abubakar,

Gwamna Aminu Bello Masari ya sake yin kira ga ‘yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani da su yi kyakkyawan amfani da kafafen wajen yada muhimmancin dorewar zaman lafiya a cikin al’umma.

Gwamna ya nuna bukatar haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan da ya halarci sallar idin karamar sallah a masallacin juma’a na Usman bin Fodio da ke Modoji a cikin birnin Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya ce kafafen watsa labarai wata babbar hanya ce ta samar da shirye-shirye a manufofi ga al’umma.

Kamar yadda ya ce babu wasu manufofi da za a cimmawa idan babu zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana cewa matsalolin tsaro a Nijeriya na bukatar hadin kan kowa da kowa domin shawo kansa.

Don haka ya yi kira ga Musulmi da sauran yan Nijeriya dasu cigaba da yin addu’o’i domin samun taimakon Allah da kuma aiki tukuru don maido da zaman lafiya a kasar nan.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki da kuma sakataren gwamnatin jiha Mustapha Muhammad Inuwa.

Sauran su ne sanannen dan kasuwan nan a jihar Katsina Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da wasu ‘yan majalissar zartarwar jih.

Babban limamin masallacin Khadi Ahmad Muhammad Batagarawa ya jagoranci raka’o’i biyu na sallar idin.

Babban limamin ya yi kira ga daukacin musulmi da su dore da yin addu’o’in domin samun rahamar Ubangiji.

Haka kuma, Khadi Ahmad Muhammad Batagarawa ya yi kira ga musulmi dasu kara gudanar daazumi na kwanaki 6 wanda ake kira da sittu shawwal domin kara samun daukaka daga Allah.

- Advertisement -