‘Yan Hijira Daga Kauyuka 25 Na Neja Na Komawa Gidajensu

- Advertisement -

‘Yan Hijira Daga Kauyuka 25 Na Neja Na Komawa Gidajensu

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Sakamakon karya lagon mahara da suka tarwatsa wasu yankunan kananan hukumomin Shiroro, Munya da Mariga na jihar Neja, yanzu haka wasu ‘yan gudun hijira solar fara komawa gidajensu a sama da kauyuka ashirin da biyar.

Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wani zama a kan tsaro da manyan jami’an tsaro da masu ruwa da tsakin a jihar, a fadar gwamnatin jihar da ke Minna.

Gwamnan ya bayyana cewar yana bibiyar sansanin ‘yan gudun hijira dan ganin halin da suke ciki wanda yanzu suna komawa gidajensu cikin kwanciyar hankali.

“Ina farin cikin sanar da cewar mafi yawan ‘yan gudun hijira na komawa kauyukansu musamman a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Mariga. Yanzu haka a kallan muna da kauyuka ashirin da biyar da mutanensu suka koma gida,” a cewar shi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, “muna samun nasara saboda gudunmawar jami’an tsaro, duk da matsalar da ake samu jami’an tsaro suna aiki bakin iyawarsu dan kawo karshen lamarin.
“Ba ina nufin ba mu da matsaloli ba ne, muna da sauran damuwa a wasu kauyukan amma jami’an tsaro suna bakin kokarinsu dan shawo kan lamarin.”
Gwamnan ya bayyana cewar sakamakon kokarin jami’an tsaro na yaki da ‘yan ta’adda soja uku solar rasa ransu a karamar hukumar Magama, inda ya kara da cewar an kashe wasu ‘yan bindigar kuma yanzu haka an samu gawar mutum biyu inda jami’an tsaron ke cigaba da yin bincike a mabuyar ‘yan bindigar inda ake kyautata zaton za a samu nasarar damke su.

Gwamnan ya ce da karin yawan jami’an tsaro daga gwamnatin tarayya a jihar, za a samu nasarar karbe sauran kauyukan da ke hannun maharan.

Gwamnan wanda ya bayyana cewar mafi yawan ‘yan gudun hijirar mutane ne da suka dogara da noma a yankunan su, inda suke da imanin komawa gidajen su dan cigaba da harkar noman su bada jimawa ba.

Gwamnan ya yaba wa kokarin manyan jami’an tsaro daga matakin tarayya da manyan shugabannin tsaro a kan yaki da ta’addanci a jihar.

Dangane da fadace fadacen matasa da makamai a cikin garin kuwa, gwamnan yace gwamnatinsa a shirye wajen hukunta duk wanda aka kama yana dauke da makami, ko yana shiga cikin fadace fadacen ko kuma yana goyon bayan fadan, domin wannan kamar daurewa sara suka gindi ne a fadar gwamnatin jihar.

” Mun tattauna akan matsalar fadace fadacen matasa a jihar nan kuma mun cin ma matsaya akan duk wanda aka samu yana dauke adda, ko wani makami dan jawo hargitsi cikin garin Minna, lallai za a hukunta shi”.

Ya bayyana yanayin da matasa ke haduwa su mamaye hanoyi suna far ma jama’a da ba su ji, ba su gani ba, duk matashin da aka cafke da sunan daba ko sara suka to kar yayi kuka da kowa, yayi kuka da kan shi.

- Advertisement -