‘Yan Garkuwa Sun Fitar Da Bidiyon Daliban Da Suka Sace A Kwalejin Afaka Har Da Mai Juna Biyu

0
364

‘Yan Garkuwa Sun Fitar Da Bidiyon Daliban Da Suka Sace A Kwalejin Afaka Har Da Mai Juna Biyu

Daga Abubakar Abba,  Kaduna

‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban Kwalejin Nazarin Gandun Daji da ke Afaka cikin jihar Kaduna,  solar fitar da faifan bidiyon daya daga cikin daliban da aka sace da take dauke da juna biyu.

dalibar ta kasance tana daya daga cikin ‘yan uwanta daliban kwalejin su 38 da aka yi garkuwar da su a cikin watan  Maris na wanann shekarar,  kamar yadda aka ruwaito batun sace su a takanin ranar 5 ga watan Afirilun wannan shekarar zuwa ranar eight ga watan.

Sai dai, masu garkuwar solar sako 10 daga cikin daliban kwalejin, inda kuma suka ci gaba da rike guda 29 a gunsu.

Bugu da kari,  tun  da farko, masu garkuwar solar bukaci sai gwamnatin jihar ta  ba su kudin fansa naira miliyan 500  kafin su sako daliban, amma gwamnatin jihar a karkashin shugabancin gwamnan Kaduna  Nasir el-Rufai ta ga za amsa yayin na ‘yan bindigar, inda hakan ya sa masu garkuwar suka bukaci iyayen daliban da su biya wadanan kudaden fansar.
Har Ila yau, a cikin faifan bidiyon mai minti hudu da sakwanni,56 da aka dauke shi da dare  a wani guri da ba a san ko a ina ba ne, an ji muryar daya daga cikin masu  garkuwar a cikin yaren Hausa  da yaren Fulfulde, yana tambayar wasu daga cikin daliban cewa,  su matso kusa da Kamara  su yi bayani.
Har Ila yau, a cikin faifan bidiyon dai, dalibar mai juna biyu wacce dan bindigar ya kira sunan ta a matsayin Hajiya ta yi kira ga iyayenta da su kubutar da su daga ‘yan bindigan.
A cewarta, “Muna kira ga iyayenmu da su taimaka su kubutar da mu daga gun mutanen nan domin mun gaji  matuka kuma ba mu da abinci”.
Ta ce,  ya zuwa yanzu,  mun shafe kwanuka 47 kuma  duk daukacinmu muna cikin rashin lafiya kuma babu abinci,  haka a fili muke kwana ko da kuma ana yin ruwan sama.
Bugu da kari, masu garkuwar solar kuma kara gabatar da wata matar wacce aka ce matar wani jami’in Soja ce da suka sato daga garinta na  Tirkania-Agwa da ke a cikin karamar hukumar  Chikun  a jihar Kaduna.
Matar ta ce, mijinta jami’in Sojan Ruwa ne da ke aiki a garin  Warri cikin jihar  Delta,  inda kuma ta yi kira ga gwamnatin  tarayya da taimaka ta sa a karbo su.
Ta bayyana cewa,  a baya,  masu garkuwar solar bukaci kudin fansa Naira 30 kafin su sako su.

What's On Your Mind?