‘Yan Daba Sun Tarwatsa ‘Yan Kungiyar Kwadagon Dake Zanga-zanga A Kaduna

- Advertisement -

‘Yan Daba Sun Tarwatsa ‘Yan Kungiyar Kwadagon Dake Zanga-zanga A Kaduna

Daga Suleiman Ibrahim

‘Yan daban da akayi haya solar tarwatsa zanga-zangar lumana da kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC) ta fara a jihar Kaduna.

A yayin da zanga-zangar ke gudana, wasu da ake zargin ‘yan daba ne solar zo a motoci biyu da KEKE NAPEP suka fara jifan masu zanga-zangar.

Wasu daga cikin ‘yan daban solar rufe fuskokinsu yayin da suke dauke da wukake da sanduna.

“Sun zo ne a cikin mota suka fara jifan ma’aikatan da ke zanga-zangar. Mutane solar fara gudu amma ma’aikatan solar sami damar korarsu, ”wani ganau ya shaida wa manema labarai.

‘Yan jarida da wasu mutane da ke kusa da wurin solar tsere daga yankin. Sai dai har yanzu ba a bayyana wadanda suka turo ‘yan daban ba, domin tarwatsa zanga-zangar.

- Advertisement -