Ranar Kirismeti: Yan Boko Haram sun kona coci a Chibok, sun hallaka mutane 6

0
41

Wasu yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane shida kuma sun banka wuta a cocin EYN (Ekklesiyar Yan’uwa a Nigeria) dake unguwar Pemi, karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

Yan ta’addan sun kai hari ranar Alhamis – daren ranar Kirismeti yayinda al’ummar garin ke shirye-shirye biki.

An kona akalla motoci shida da gidaje biyar mallakin cocin, TheCable ta samu bayani daga wasu mazauna garin ranar Juma’a.

“Yan ta’addan sun zo misalin karfe 5:30 na yamma ta Gogombi,” daya daga cikin mutan kauyen ya fada.

Soyayya Gamon Jini ! Wannan Tsoho Ya Roki Allah Ya mallaka masa Hadiza Gabon

“Sun zo a rabe-rabe biyu. Na farko sun shigo kan babura yayinda na biyun suka zo cikin manyan motoci. Shiga kauyensu ke da wuya suka fara harbin cocin EYN.”

“Sannan suka bankawa cocin wuta. Hakazalika suka kona motoci shida da wasu gidaje biyar dake makwabtaka da cocin.”

“Wasu cikinmu sun gudu cikin daji, amma an kashe mutane a harin. Kiristoci na shirin addu’o’in Kirismeti a cocin da safen nan.”

An samu rahoton cewa sai bayan awanni da yan ta’addan suka tafi Sojoji suka iso.

What's On Your Mind?