Yan Boko Haram sun kafa sababbin sansanoni, sun boye a Adamawa da Yobe

0
25

Bayanan da jami’an tsaro su ke samu a Najeriya shi ne ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kafa wasu sababbin sansanoni a Arewa maso gabas.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar 11 ga watan Fubrairu, 2021, ta tabbatar da wannan lamari.

Rahoton ya ce ‘yan ta’addan wanda su ka shafe shekara da shekaru su na ta barna a yankin sun samu wasu mafaka inda za su rika boye wa jami’an tsaro.

Ana zargin cewa ‘yan ta’addan na kungiyar Boko Haram sun kafa wadannan sansanoni a yankin Geidam da ke jihar Yobe, da wani bangare a jihar Adamawa.

 Yan Boko Haram sun kafa sababbin sansanoni, sun boye a Adamawa da Yobe

Bayan rashin nasarar aure har biyu Fati Muhd ta bayyana burin ta a duniya

Majiyar jami’an tsaro ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’addan sun tare a wasu garuruwan Yobe da su ka hada da Tarmuwa da Yunusari.

A jihar Adamawa kuwa, ‘yan Boko Haram sun pretend ne a yankin Mubi, Madagali da kuma Gombi.

Karamar hukumar Madagali ta na kan iyaka ne da kasar Kamaru. A shekarun baya, ‘yan Boko Haram sun kai munanan hari a garuruwan Gombi da Mubi.

Ko a ‘yan kwanakin bayan nan, ‘yan ta’addan sun auka wa garin Geidam, su ka yi nasarar yin awon gaba da wasu jami’ai uku na hukumar kwastam na kasa.

‘Yan Boko Haram sun dauki akalla kimanin sa’a biyu su na ta’adi a karamar hukumar Geidam, mahaifar tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Ibrahim Geidam.

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya zargi sojojin Najeriya da ruruta wutar ta’addanci a kasar nan, ya ce sun hana matsalar ta kare.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce matukar jami’an tsaro su na amfana da biliyoyin kudin da ake warewa saboda yaki da ta’addanci, ba za a dage domin a samu tsaro ba.

Gumi yace ‘yan bindiga sun shirya tsaf domin ajiye makamai amma bisa wasu sharuda.

What's On Your Mind?