Yan Boko Haram na horar da makiyaya tare da karbar shanu a matsayin haraji, Rahoto

0
201

Yan Boko Haram na horar da makiyaya tare da karbar shanu a matsayin haraji, Rahoto

Kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da ‘yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jihar Yobe inda ‘yan Boko Haram ke horar da makiyayan dabarun yaki.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace ‘yan ta’addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.

An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.

Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

“Horar da makiyaya da karbar haraji daga wurinsu ba yau aka fara ba a garin Geidam dake jihar Yobe. ‘Yan ta’addan na bukatar abinci da suka hada da nama kuma suna horar da makiyaya a kauyukan Gonisaleri, Dawayya da Abari duk a karamar hukumar Geidam,” majiya daga rundunar soji ta sanar.

“‘Yan ta’addan na karbar sa daya a duk shanu 40 a matsayin haraji, suna bada hatimi tare da shaidar biya ga makiyaya. Abun tamkar a shirye ake yinsa,” ya sake bayyanawa.

A wani labari na daban, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da abu mafi alheri da ya taba faruwa a Najeriya.

A yayin tattaunawa a shirin siyasarmu a yau wacce gidan talabijin na Channels yayi, gwamnan yace an samu manyan nasarori yayin mulkin.

Mai gabatarwa ya tambaya gwamnan ko ya sakankance da abinda takwaransa na APC yace, sai gwamnan yace: “Na yadda gaskiya, na amince dari bisa dari. Na san abinda na gada, na san matsalolin da na shiga. A wani lokaci na so tserewa. Amma da babu taimakon shugaban kasa Buhari, ba za mu daga kawunanmu a matsayin gwamnoni ba.”

What's On Your Mind?