‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kashe Ragowar Daliban Jami’ar Greenfield Yau Talata

0
88

‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kashe Ragowar Daliban Jami’ar Greenfield Yau Talata

Daga Yusuf Shu’aibu,

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban jami’an Greenfield guda 23 a kan babban haryar Kaduna zuwa Abuja, solar yi barazanar kashe sauran daliban idan gwamnatin ba ta biya kudin fansa ba kafin ranar Talata. Wadannan ‘yan bindiga solar sace daliban jami’an ne a wani farmaki da suka kai a ranar 20 ga watan Afrilu shekarar 2021. Masu garkuwan solar kashe biyar daga cikin daliban, ida a yanzu suke yin barazanar a kan za su kashe sauran daliban da ke hannunsu idan ba a kai musu kudin fansa ba kafin ranar Talata.

A wani fira da sashin Hausa na gidan rediyon Amurka (VOA) ya yi da su , ‘yan bindigan solar bayyana cewa solar kashe dalibai guda biyar din da suka yi garkuwa da su a ranar 20 ga watan Afrilu ne sakamakon gazawar gwamnatin. ‘Yan bindigan dai solar bukaci a ba su kudin fansa na naira miliyan 800 bayan da suka yi garkuwa da daliban, amma bayan kwanaki uku da ba a biya musu bukatarsu ba, solar kashe dalibai guda uku, inda suka kashe guda biyu bayan kwanaki kadan.

Da yake zantawa da sashen Hausa na VOA, shugaban ‘yan bindigar mai suna Sani Idris Jalingo, ya bayyana cewa idan gwamnatin Jihar Kaduna ko kuma iyayan daliban suka kasa biyan kudi fansa na miliyan 100 tare da babura guda 10 sabbin kirar Honda kafin nan da ranar Talata, za su kashe sauran daliban. Jalingo ya bayyana cewa, iyayen daliban solar biya naira miliyan 55, amma solar yi amfani da wannan kudi wajen ciyar da daliban.

“Mun ji gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru el-Rufa’i yana cewa ba zai biya wani kudin fansa ga duk wasu ‘yan bindiga, domin kar su kara sayan makamai. Mun nuna gazawar gwamnatin Nijeriya shi ya sa muka kashe daliban,” in ji shi.

dalibai guda biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su solar yi magana, inda suka roki gwamnatin da iyayansu da su dauki wannan barazana da matukar mahimmanci.

daya daga cikin daliban wanda shi jikan tsohon sarki Zazzau, Shehu Idris ya yi kira da gwamnatin da ta sasanta da masu garkuwa.

“Suna cika duk wani alkawarin da suka yi, saboda solar kashe wasu daga cikin mu,” in ji Idris.

Idan ba a manta ba dai an tsinci gawar daliban guda uku wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 23 ga watan Afrilu wanda ya haddasa tashin hankali a cikin garin Kaduna. Bayan kwanakin uku, ‘yan bindigar solar sake kashe karin dalibai guda biyu, wanda ya sa adadin daliban da suka kashe ya kai guda shida. Saboda solar kashe wani ma’aikacin makarantar lokacin da suke kokarin yin garkuwa da daliban.

What's On Your Mind?