Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

0
10

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da jami’an yan sanda 18 a Farin-Ruwa, hanyar Birnin Gwari – Funtua a jihar Kaduna, Arewa maso yammacin Najeriya.

SaharaReporters ta ruwaito cewa yan sandan na hanyarsu ta zuwa Kano daga Minna, jihar Neja ranar Juma’a lokacin da aka bude musu wuta.

Amma majiyoyi sun bayyana cewa Sojoji sun ceto kimanin yan sanda 10 a Maganda ranar Asabar.

Shugaban kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU), Barista Salisu Haruna, ya tabbatar da harin a wani jawabi.

Haruna ya ce yan sandan dake Dogon Dawa sun samu labarin hakan.

Yace, “Kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU) ta ruwaito cewa har yanzu ba’a san idan jami’an yan sanda 18 da aka kaiwa hari a hanyar Birnin-Gwari Funtuai ranar Juma’a, 15 ga watan Junairu, 2021, suke ba.

“Yan sandan 18, wadanda ke kula da hanyar Birnin Gwari Funtua, sun gamu da hari ranar Juma’a. A lokacin da ake kawo wannan rahoto, bamu san adadin wadanda abin ya shafa ba.”

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

“Masu idanuwan shaida na tunanin wasu cikin yan sandan sun rasa rayukansa yayinda wasu sun bace cikin daji.”

Ka rushe kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 babu abinda suke sai satar kudi~PDP ga Buhari

“Rahotannin sun tabbatar da cewa yan sanda biyu sun yi waya domin sanar da gida cewa an kai musu hari amma basu san inda suke ba.”

“BEPU na kira ga gwamnati, wacce aka saurawa hakkin kula da rayukanmu da dukiyoyinmu, ta mike tsaye domin yaki da rashin tsaro har sai an samu nasara.”

A wani labarin daban, rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.

 444 total views,  3 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here