Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Sarki

0
163

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Sarki

Wasu ‘yan bindiga da ba’a gane ko suwaye ba sun farmaki wani sarkin gargajiya a Jihar Ogun yayin da yake dawo wa daga wani wuri. Wani na kusa da wanda aka sace ya ce mutanen sun farmaki Omotayo ne kan hanyarsa ta komawa gida.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai ba su ba da cikakken bayani ba domin suna kan bincike. ‘Yan bindigar da ba’a gano ko suwaye ba har yanzun, sun kai farmakin ne kai tsaye kan magajin garin Imope Ijebu dake Karamar Hukumar Ijebu ta Arewa mai suna, Chief Kolawole Omotayo, kuma suka yi awon gaba da shi.

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

Amma Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an sace Omotayo ne a kan hanyar Oke Eri-Imope, yana kan hanyarsa ta komawa gida daga Ijebu-Ode, inda ya je domin sayo wani abu. Wani na kusa da magajin garin ya fada wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun harbi tayoyin motar da yake ciki guda biyu, wanda take da lambar rijista ‘WJ9’.

Sun kuma fasa injin motar da harsashi, wanda hakan ya basu dama suka cimmasa suka fito da shi daga cikin motar kuma suka tasa shi zuwa cikin daji.

Jami’i mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Oyeyemi, ya ce ba zai iya ba da bayanin yadda lamarin ya faru ba amma ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda na gunadar da bincike a kan lamarin. Rahoto ya bayyana cewa mutumin da aka sace shi ne shugaban inyamurai na garin Ijebu.

What's On Your Mind?