Yan bindiga sun sheke ‘yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

0
155

Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

Yan bindiga sun sheke ‘yan sanda uku a sabon harin da suka kai karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

The Cable ta gano cewa ‘yan sanda da aka kashe a safiyar Litinin suna kan titi ne yayin da suke duba motoci masu wucewa.

An gano cewa ‘yan sandan sun kai harin sannan suka yi awon gaba da bindigogin jami’an tsaron.

Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

‘Yan sandan da aka kashe sun hada da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi.

Ude Chukwu, mataimakin gwamnan jihar, ya kushe wannan harin yayin da ya kai ziyara yankin bayan sa’o’i kadan da aukuwar lamarin.

Ya kara tabbatarwa da mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta tura abubuwan da ake bukata.

Cigaban yazo ne kasa da wata daya bayan kashe wani jami’in dan sanda da aka yi a jihar bayan ‘yan bindiga sun kutsa Aba.

‘Yan bindigan sun yi awon gaba da makamai daga ofishin ‘yan sandan.

Lamarin da ya faru na nuna hauhawar rashin tsaro da kuma harin da ake kaiwa jami’an tsaro a yankin kudancin kasar nan.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karba bakuncin Oladimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai da Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun a fadarsa dake Abuja.

Bankole da Daniel cikin kwanakin nan ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Yayin kai ziyarar fadar shugaban kasa, sun samu rakiyar Mai Mala Buni, Mohammed Badaru da Atiku Bagudu, gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi.

What's On Your Mind?