‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane Yayin Ibadar Lahadi A Kaduna

0
119

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane Yayin Ibadar Lahadi A Kaduna

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Da misalin karfe tara na safiyar jiya Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka auka cikin Cocin Haske Baptist da ke yankin Manini a Unguwar Sabon Tasha a karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna, inda suka kashe wani a mutum daya da aka ce  likita ne a  yayin da  gudanar da ibada sannan suka yi awon gaba da wasu da dama.

An ruwaito cewa, ‘yan bindigar solar kuma raunata wasu mutanen daban a cocin.

Wani ganau wanda ya tsallake rijiya da baya Mista Yakubu Bala ya bayyana cewa, ‘yan bindigar solar aka cikin Cocin ne dauke da muggan makamai.

A cewarsa, ‘yan bindigan solar yi dirar mikiya a cocin inda suka fara harbin masu gudanar da ibadar da ke a cikin Cocin, kowa ya yi ta kansa.

Ya ce,  wanda aka kashe din, Shi ne Dakta, Zakariah Dogo Yaro, babban likita  a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da kula da harkokon cikin gida Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin.

karamar hukumar ta Chikun dai, ta jima tana fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

In za a iya tunawa, ko a cikin watan Fabirairun wannan shekarar, wasu ‘yan bindiga solar kai farmaki a Cocin Holy Household dake a kauyen Kikwari  cikin karamar hukumar Kajuru, inda kuma suka banka wa Cocin wuta tare da kone wasu gidaje biyu.
……………..

What's On Your Mind?