Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

0
33

Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kaigar Malamai da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina

– Maharan sun kuma yi garkuwa da Hakimi kauyen, matan aure, yan mata da kuma wasu kananan yara

– Zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin yan sanda sport da lamarin ba Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a daren ranar Litinin, sun yi garkuwa da hakimin kauyen Kaigar Malamai, a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina tare da wasu (*15*) 15.

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa yan bindigan su da yawa sun kai farmaki kauyen da misalin tsakar dare a ranar Litinin sannan suka shafe tsawon sa’o’i da dama suna aiki inda daga baya suka tafi da mutanen.

Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

Yan bindiga sun sace basarake da wasu (*15*) 15 a kauyen Katsina Hoto: @MobilePunch Supply: Twitter “Sun kai farmaki kauyenmu, Unguwar Malamai da misalin karfe 11:45 na tare sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

Wuff ! Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa’ar mahaifiyarsa yayi murnar rabuwa da ita

“Sun yi garkuwa da (*15*) 16 ciki harda hakimin kauyen, Maiunguwa Kabir, matan aure shida, yan mata uku da kuma yara shida,” in ji shi kamar yadda jaridar Every day Belief ta ruwaito.

Sai dai, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, bai rigada ya tabbatar da lamarin ba amma ya yi alkawarin dawowa ga manema labarai wanda hakan bai samu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani labarin, wani jami’in dan sanda kuma dogarin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane amma ya samu kubuta.

Dan sandan, wanda dan asalin jihar Nasarawa ne, yana kan hanyar zuwa Abuja daga Doma a karshen makon da ya gabata akayi garkuwa da shi a Ikari, wani kauye dake Gudi karkashin karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.

Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na dare yayinda yan bindigan suka tare hanya, suka yi fashi, sannan sukayi awon gaba da mutane hudu.

What's On Your Mind?