Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

0
309

Lawal Musa, shugaban al'ummar Fulani a karamar hukumar Kajuru da ke Kaduna, ya rasa ransa sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai, The Cable ta ruwaito.  Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.  Musa, wanda aka fi sani da suna "Alhaji Maijama'a", an ba da rahoton kashe shi a daren Lahadi.  Kwamishinan ya bayyana cewa Musa yana kan babur tare da dan uwansa, kwasam ‘yan bindigan suka bude musu wuta.

Lawal Musa, shugaban al’ummar Fulani a karamar hukumar Kajuru da ke Kaduna, ya rasa ransa sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai, The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Musa, wanda aka fi sani da suna “Alhaji Maijama’a”, an ba da rahoton kashe shi a daren Lahadi.

Kwamishinan ya bayyana cewa Musa yana kan babur tare da dan uwansa, kwasam ‘yan bindigan suka bude musu wuta.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban al’ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru, Alhaji Lawal Musa, wanda aka fi sani da Alhaji Maijama’a, a daren ranar Lahadi,” in ji sanarwar.

“Jami’an tsaro ne suka sanar da wannan ga Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi.

“Alhaji Lawal Musa ya kasance shugaban al’ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru wanda ya yi aiki kafada da kafada da sauran shugabannin al’ummar wajen cimma nasarar kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

“Wasu ‘yan bindiga sun kashe Alhaji Lawal Musa a mazauninsa, a gaban danginsa. Yana kan babur tare da babban wansa, Alhaji Gide Musa, lokacin da wasu mahara suka bude musu wuta.

“Alhaji Gide Musa ya tsere da raunin harbin bindiga, yayin da ‘yan bindigan suka rike Alhaji Maijama’a suka yi masa yankan rago har lahira.

“Tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Dan uwan ​​nasa yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba. ”

Aruwan ya bayyana gudummawar da Musa ya bayar a matsayin “kayan aiki don sake bude kasuwar mako-mako ta Doka, sake dawo da hada-hada cikin lumana a wuraren ibada da aka yi watsi da su da kuma sake dawo da kiwo da noma a babban yankin Doka”

Kwamishinan ya kara da cewa Nasir El-Rufai, gwamnan jihar ta Kaduna, ya yi Allah wadai da lamarin kuma ya aike da ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Haka kuma an ce El-Rufai ya bayyana marigayi shugaban na Fulani a matsayin “shugaba nagari kuma mai kishin zaman lafiya”.

A wani labarin, Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, sun bada wa’adin awanni 48 ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya don ceton ’ya’yansu.

Wannan ya kasance daidai lokacin da iyayen, cikin kuka, suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i da shugabannin duniya da su tabbatar da hanzarta kubutar da ‘ya’yansu daga ‘yan bindiga.

What's On Your Mind?