Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mutum 18 a Kebbi

0
124
  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 4, sun kuma yi garkuwa da mutane 18 a watan jiya a masarautar Zuru ta jihar Kebbi

  • Shugaban IAZE, Sheikh A. G Mika’il ya sanarwa manema labarai hakan a ranar 25 ga watan Oktoba 2020

  • Ya roki jami’an tsaro da su taimaka su kawo dauki kuma su ceto rayuwar wadanda aka yi garkuwa da su

Shugaban IAZE, Sheikh A. G Mika’il ya sanar da manema labarai a birnin Kebbi yadda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da mutane 18 a jihar Kebbi.

Ya roki jami’an tsaro da su taimaka su cetosu daga hannun ‘yan bindigan.

Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mutum 18 a Kebbi

A ranar 25 ga watan Satumbar 2020, ‘yan bindiga sun kai hari, inda suka kashe (*18*) 1 a Akawo, suka kuma kashe mutane 2 a ‘Yar Kasuwa.

Sun kuma yi garkuwa da mutane 5 a karamar hukumar Fakai a jihar Kebbi.

Sun kara da yin garkuwa da mutane 3 a karamar hukumar Zuru, sunyi garkuwa da mutane 3 a Senchi, 1 a Udun-Kudu, 1 kuma a Danko, sun kashe (*18*) daya a karamar hukumar Wasagu kuma sunyi garkuwa da mutane 9.

Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

“Don haka muna rokon hukumomin tsaro da su cigaba da bada tsaro isasshe kuma su ceto rayuwar wadanda sukayi garkuwa da mutane,” yace

A wani labari na daban, an ceto ma’aikatan gwamnatin jihar Borno 5 da ‘yan kungiyar ISWAP suka yi garkuwa dasu watan da ya gabata.

Anyi garkuwa da ma’aikatan RRR dinne, yayin da suke kan hanya tsakanin Maiduguri da Monguno. Ma’aikatan 5 sun bayyana a wani bidiyo ne jiya suna neman taimakon gwamnatin jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun yi ikirarin kai wa ma’aikatan gwamnati farmaki akan aikin da suke yi wa “makiya addinin musulinci.”

‘Yan ta’addan sun yi ikirarin hakan kafin su kai wa ma’aikatan farmaki, inda suka kama wasu ma’aikatan tsaro a watan Augusta.

What's On Your Mind?