Yan bindiga sun kashe jami’in kwastam da wasu 9 a Katsina

0
64

‘Yan (*9*) sun kashe jami’in hukumar yaki da masu fasakwabri wato kwastam yayin da ya ke bakin aikinsa a kauyen Dan Arau da ke babban titin Katsina/Jibya.

Sun kashe Garba Nasiru, mai mukamin mataimakin sufritanda ne yayin wani hari mai ban mamaki da suka kai a ranar Juma’a sannan suka tafi da bindigarsa AK 47.

Yan bindiga sun kashe jami'in kwastam da wasu 9 a Katsina

The Punch ta ruwaito cewa sai da aka yi bata-kashi da jami’an tsaro sannan suka yi nasarar kwato gawarsa daga hannun ‘yan bindigan inda suka tsere suka shiga cikin daji.

Rahotanni sun nuna cewa tuni an yi wa jami’in jana’iza bisa koyarwar addinin musulunci duk da cewa kokarin da aka yi na ji ta bakin kakakin rundunar na Katsina bai yi wu ba.

Amma kakakin ‘yan sanda na jihar Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin duk da cewa bai yi karin bayani ba.

Fatima Nuhu Ribaɗo Amarya Dan Atiku Abubakar ta yi martani

Ya ce, “Eh, da gaske ne. ‘Yan (*9*) sun kashe jami’in kwastam a kauyen Dan Arau amma ku tuntubi hukumar kwastam domin karin bayani”.

A wani labari mai kama da wannan da ya faru a yammacin ranar Juma’a, ‘yan (*9*) sun kashe mutum tara a kauyen Tsauwa da ke karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da afkuwar lamarin.

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma’aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

What's On Your Mind?