Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun yi kisa, sun tafka barna

0
7

Wasu ‘yan bindiga dadi sun kai hari garin Magarya da ke yankin karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara, a ranar Talata.

Garin Magarya ne mahaifar shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.

“Wasu ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun dira garin Magarya tare da budewa jama’a wuta.

Sun hallaka mutane biyu nan take, sun lalata dumbin dukiya tare da yin awon gaba da shanu fiye da 100 bayan sun kone rumbunan da jama’a suka adana abinci,” kamar yadda wani dan majalisa ya shaidawa Day by day Belief.

Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun yi kisa, sun tafka barna

An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

A ranar Laraba ne Honarabul Muazu ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati zuwa garin Magarya domin jajantawa jama’a akan abinda ya faru.

Dagacin Magarya ya zagaya da tawagar jami’an domin su ganewa idanuwansu irin barnar da ‘yan bindiga suka tafka a garin.

A yayin da yake gabatar da jawabin jaje, Honarabul Muazu ya dauki alkawarin za’a turo karin jami’an tsaro zuwa yankin domin zakulo ‘yan ta’adda.

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda ‘yan ta’adda ke salwantar da rayukan jama’a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda a cikin wannan shekarar, 2021.

 204 total views,  3 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here