Hotuna: Yan bindiga 7 sun ajiye makamai sun mika wuya a Zamfara

0
13

Wasu yan bindiga su bakwai sun rungumi zaman lafiya sun ajiye makamai sun mika wuya a jihar Zammfara.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ne ya karbe su a gidan gwamnati da ke Gusau kamar yadda TVC ta ruwaito.

Yan bindiga 7 sun ajiye makamai sun mika wuya a Zamfara

Yan bindiga 7 sun ajiye makamai sun mika wuya a Zamfara

Wasu ‘yan matan Chibok sun sake tsere wa daga hannun Boko Haram

Tubabbin yan bindigan sun mika makamansu da suka hada da bindigu kirar AK 47, alburusai da harsasai fiye da dubu daya.

Wasu daga cikin sarakuna a jihar ta Zamfara sun hallarci taron na mika makaman da rungumar zaman lafiya.

Kazalika, wakilan hukumomin tsaro da suka hada da rundunar sojoji da wasu hukumomin sun hallarci taron.

What's On Your Mind?