‘Yan Arewa Su Daina Bari Ana Amfani Da Su Wajen Zubar Da Mutuncin Shugabanninsu

- Advertisement -

‘Yan Arewa Su Daina Bari Ana Amfani Da Su Wajen Zubar Da Mutuncin Shugabanninsu

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An nemi al’ummar arewa da su daina barin batagari na anfani da su wajen zubar da kimar shugabannin su, domin hakan bai haifar da komai face rarrabuwar kawuna na mayar da yankin baya.

Alhaji Awaisu Muhammad Wanna ne yayi kiran musamman ganin yadda ake ta tada jijiyar wuya a kafofin sadarwa kan kazafin da aka yiwa tsohon shugaban kasa Janar Abdussalam Abubakar na alaka da jirgin da ake cewa an kama yana kaiwa ‘yan ta’adda abinci da makamai.

Abin dariya da rashin tunani ga masu kaga ire-iren wadannan labaran karyar ko me ye ribarsu ga irin wannan karyar. Kar fa mu manta cewar Janar Abdussalam na daya daga cikin tsoffin shugabannin kasa masu daraja, domin a siyasar duniya yau yana daya daga cikin dattijan da in matsala ta taso ana anfani da su wajen walwale shi. Ta ina zai tsaya yana daurewa ‘yan ta’adda gindi, da mulkin yake so da yanzu yana kai, domin ya samu mulkin a lokacin da bai tsammaninsa ba amma yace cikin watanni tara zai mika mulki a hannun zababbiyar gwamnatin farar hula kuma kowa shaida ne akan hakan.

Ina ganin rahoton nan da ake yadawa, makiya arewan nan da suka kashe su marigayi sardauna su ke cigaba da bibiyan manyan mu, kafin Janar Abdussalam ba abinda ba su cewa Janar Babangida ba, saboda ina kiran ‘yan arewa da babban murya da mu tabbatar masu cewar kan mage ya waye, duk wani tuggun da zasu rika yiwa manyan mu na arewa muna kallon su kuma ba za mu kyale ba.

Maganar maharan nan ba yakin kasa da kasa ba ne ba fa, wata kabila ce ta dauke makami ta sari ka noke, wanda kuma jami’an tsaro na bakin kokarin su akai. Ni kaina ina magana da manyan jami’an tsaro lokaci zuwa lokaci ina jin irin kokarin da su ke yi, ko Sheihk Ahmed Gummi da ke shigarsu dan yana kabilarsu ne, saboda ina jawo hankalin jama’a da su yi watsi ire-iren rahotannin da su ke gani a yanar gizo ko jaridu dan yin batanci ga manyan mu.

Kwanakin baya solar ruwaito cewar wai an kama jirgin sama a yankin Erena da wasu sojoji a ciki da ake zargin suna taimakawa ‘yan ta’adda wanda zuwa yanzu ko hoton jirgin ba a taba gani ba, sannan yanzu solar dauko wani tsohon hoton jirgin sama wai na Abdussalam ne, wannan duk batanci ne kawai.

Idan ka zargi Abdussalam da IBB wajen kin sanya baki dan kawo karshen wannan ta’addancin a jihar nan, to me ye matsayin manyan jihar Katsina, Zamfara da abin ya faro wurin su har ya kwararo nan, ko kuma shekaru sha uku na Boko Haram a kasar Maiduguri, maganar gaskiya annoba ce koma in ce wata jarabawa ce ta fado wa kasar nan da sai dai mu yi ta addu’ar ganin karshen sa.

- Advertisement -