Yajin Aikin Gargadi: Yau Kaduna Za Ta Tsaya Cik Yayin Da…

- Advertisement -

Yajin Aikin Gargadi: Yau Kaduna Za Ta Tsaya Cik Yayin Da…

Ma’aikatan Lantarki, Sufuri Da Ruwa Suka Ba Da Hadin Kai
Shugabannin Kwadago Na Kasa Suka Yi Dirar Mikiya
Sharadin Sulhu Shi Ne Dawo Da Ma’aikata Sama Da 6,000 Da Aka Kora – NLC
Duk Wanda Ya Shiga Yajin Aiki A Bakin Aikinsa –Gwamnatin Jihar

Daga Shehu Yahaya,

Biyo bayan korar ma’aikata sama da dubu shida da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed el-Rufai ta yi, kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa dukkanin ma‘aikatun gwamnati da makarantu da asibitoci za su kasance a rufe sai dai ‘yan kasuwa kawai wadanda yajin aikin bai shafa ba.

kungiyar ta ‘yan kwadago ta tsunduma wannan yajin aikin ne a jiya Lahadi, domin tursasa gwamnatin Jihar Kaduna dawo da ma’aikatan da ta kora aiki ba Bisa ka’ida ba da kuma biyan wasu hakkokinsu.

Shiga yajin aikin ya durkusar da tattalin arzikin jihar bisa ganin duk hada-hadar kasuwanci solar yi tsaye cak yayin da wakilinmu ya leka kwaryar cikin garin Kaduna wadda aka sani da hada-hada sosai.

Wakilinmu da ya kewaya wasu wurare ya tarar da hatta gidajen sayar da man fetur duk a rufe suke baya ga ma’aikatun gwamnatin wadanda su ma a garkame suke duk kuwa da cewa gwamnatin ta bayar da sanarwa ajiye littafin rubuta suna ga duk ma’aikacin da ya zo aiki domin tantance wadanda suka zo aiki.

Shiga yajin aikin ya jefa Jihar Kaduna cikin mawuyacin hali na durkushewar tattalin arzikin baki daya.

Tun a daren ranar Asabar Kamfanin Samar da Wutar lantarki ta Kaduna (KEDCO) ya fara yajin aikin inda ya jefa garin Kaduna cikin duhu na rashin wutar lantarki.

Su ma ma’aikatan sufurin jiragen sama da sufurin ababen hawa duk solar shiga yajin aikin.

Haka ita ma hukumar samar da ruwan sha ita ma ta bi sahun kungiyar kwadago na shiga yajin aikin inda ma’aikatanta suka dauke ruwan sha.

Kusan duk bangarorin ci gaban jihar ba sa aiki solar tsaya cak lamarin da ke nuna tasirin shiga yajin aikin.

A zantawarta da wakilinmu ya yi da sakatariyar NL reshen Kaduna, Christiana John Bawa, jim kadan bayan kammala taron manema labarai a sakatariyar kungiyar ta Jihar Kaduna, ta ce shiga yajin aikin ya zama wajibi duba da yadda gwamnatin Jihar Kaduna ba ta damu da rayuwar ma’aikata ba.

Ta ce a fadin kasar nan Kaduna ce ba ta damu da hakkokin ma’aikaci ba, inda take sallamar su ba tare da biyansu hakkokinsu

“Idan ba’a manta ba gwamnatin Jihar Kaduna ta kori ma’aikata sama da guda dubu 30 a shekarar 2016 wadanda har yanzu ba ta biya su hakkokinsu ba”

“A tarihin Nijeriya babu wata gwamnatin da ta kori ma’aikata kamar Gwamnatin el-Rufai  saboda baka lokaci ya yi da za mu tabbatar wa duniya cewa gwamnatin Jihar Kaduna ba ta kaunar ma’aikata wacce kuma take fakewa da yiwa tsarin aikin gwamnatin gyara tana korar ma’aikata ba tare da bin ka’ida ba” in ji ta.

Akan hakan ta bukaci daukacin ma’aikata a jihar da su tsunduma cikin yajin aikin kuma su yi Watsi da sanarwar gwamnatin jihar na cewa babu yajin aikin.

Christiana John Bawa, ta kara da cewa duk kungiyoyin da Suke da alka da kungiyar kwadago ta NLC a jihar za su tsunduma cikin yajin aikin. Tana mai cewa zasu fara yajin aikin babu gudu babu ja da baya.

Hakazalkka, a jiya Lahadi duk shugabannin kungiyar kwadago na kasa bisa jagorancin Ayuba Waba suka shigo cikin garin Kaduna domin halartar zaman yajin aikin inda suka ce matsalar Jihar Kaduna matsalar Nijeriya ce.

 

A zantawarsa da wakilinmu Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomin Jihar Kaduna Alhaji Jafaru Sani, ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ba ta amince da wani ya shiga yajin aikin ba kuma rashin bin umar Umarnin gwamnatin laifi ne.

 

Jafaru Sani, ya yi watsi da yunkurin kungiyar kwadago na shiga yajin aiki yana mai jan hankalinsu na su janye.

… Sharadin Sulhu Shi Ne Dawo Da Ma’aikata Sama Da 6,000 Da Aka Kora – Ayuba Magaji

 

 

A halin da ake ciki kuma, Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen Jihar Kaduna Kwamaredd Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta biya ma’aikata sama da 2000 albashin watan Afrilun da ya gabata a fadin jihar ba.

 

Ayuba Suleiman, ya ce irin matakan da gwamnatin jihar Kaduna take dauka a kan ma’aikata a jihar ya saba wa tsari da dokar ma’aikata a kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu, inda ya ce babu wata barazana da gwamnatin jihar za ta yi a kan hana su gudanar da shiga yajin aikin a yau.

 

Ya ce a fadin kasar nan gwamnatin Jihar Kaduna ce kadai take wulakanta rayuwar ma’aikata, wanda kungiyar kwadago ta NLC ba za ta lamunta ba.

 

Ayuba ya ce muddin gwamnatin jihar tana bukatar su janye yajin aikin, sai ta dawo da sama da guda dubu shida da ta kora aiki da kuma biyan wasu hakkokinsu na sallamar aiki yana mai cewa kofarsu a bude take domin sulhu da gwamnatin wanda da kamar wuya.

Akan hakan, ya yi kira ga jami’an tsaro da kada su yarda gwamnatin jihar ta yi amfani dasu wajen hana su zanga-zagar inda ya ce suna da labarin cewa gwamnatin za ta yi amfani da su wajen hana yajin aikin.

Ya kuma bukaci daukacin ma’aikata da su zauna a gida har sai yadda hali ya yi. Ya ce shiga yajin aikin ba-gudu-babu-ja-da-baya.

- Advertisement -