Yahaya Bello Ga Gwamnonin Kudu: Dukkanmu Mun Gaza, A Daina Dora Wa Buhari Laifi Shi Kadai 

- Advertisement -

Yahaya Bello Ga Gwamnonin Kudu: Dukkanmu Mun Gaza, A Daina Dora Wa Buhari Laifi Shi Kadai 

Daga Yusuf Shu’aibu,

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince da gazawar gwamnati a dukkan bangarori, yana mai gargadi ga gwamnonin Kudu recreation da fada da shugaba kasa Muhammadu Buhari ko kuma dora alhakkin hakan ga gwamnatin tarayya. Bello ya yi magana ne yayin da yake nunawa a shirin ‘Siyasar Yau’ ta gidan talabijin din Channels, yana mai gargadin takwarorinsa na jihohin Kudancin kasar nan da su yi hankali da maganganunsu don ka da su zafafa batun.

Ya ce, “bari in yi gargadi ga kowannenmu, shugabanni a dukkan bangarorin da suka hada da gwamnoni da dukkan shugabannin a duk fadin Nijeriya cewa, ya kamata mu yi taka tsantsan recreation da kalaman da muke amfani da su.

“Lokacin da muke magana kan tsaro, hadin kai da kuma dunkulewar kasa Nijeriya, a matsayinmu na shugabanni da‘yan siyasa, ya kamata mu kiyaye recreation da kalaman da muke amfani da su yayin da muke magana a kan wadannan batutuwa da dama.

“Lokacin da boye ko kuma lokacin da ya zama kamar kuna fada ne da shugaba Muhammadu Buhari, mahaifinmu kuma shugabanmu, dukkanmu muna ganin ba dai-dai ba ne saboda mun kai ga inda muke a yau sakamakon rashin kyakkyawan tsari na gwamnatocin da suka gabata.

“An samu gazawar gama gari a dukkan bangarorin gwamnati, don haka ka da mu zargi kawai gwamnatin tarayya ko shugaba, mu zargi kawunanmu,” in jib shi.

Haka kuma, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya kara jaddada cewa, mafi yawancin ‘yan Nijeriya ne ke ta rokonsa da ya fito takarar shugabancin kasa nan a shekarar 2023, saboda ya cancanta kuma ba zai bai wa ‘yan Nijeriya kunya ba. Gwamnan kara da ya ce, babu shakka akwai abin da mata da matasa suka hango a tare da shi ne wanda ya sa suke ta wannan tururuwar a gare shi na ya fito takarar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa. A cewarsa, kasar Nijeriya tana bukatar tsayayyen mutum da zai iya hada kan jama’a, kuma babu shakka zai iya hakan.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce, dukkan ‘yan Nijeriya ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa nan a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Lokacin jawabisa a ranar Juma’a wajen shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai ba da ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa. Gwamnan ya ce, ‘yan Nijeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasar Nijeriya.

“Matasa da mata tare da dukkan ‘yan Nijeriya suke rokona da in tsaya takarar shugaban kasa a 2023. Kuma na yadda cewa lokaci ya yi da zan duba ko zan iya. Waye zai iya hada kan kasar nan? Ina tunanin suna ganin wani abu a tare da ni ne shi ya sa suke son in zo in hada kan kasar nan kuma in gyarata.

“Nan ba da dadewa zan amsa musu. Ina kira ga kowa da kowa da ke yi min wannan kiran na takarar shugabancin kasa da su yi hakuri.

“Har yanzu akwai aikin da nake yi kuma da izinin Ubangiji, ba zan ba ku kunya ba idan lokacin yanke hukuncin zan fito takara ko ba zan fito ba ya yi,” in ji shi.

- Advertisement -