Yahaya Aminu Sharif: Kotun Daukaka Ƙara ta ce a koma kotun Musulunci Wanda Yayi Ɓatacin Ga Manzon Allah (S.a.w)

- Advertisement -

Wata Kotun Daukaka Kara da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke hukunci kan wasu matasa biyu da ake zargi da yin batanci fa Annabi S.A.W.

Kotun ta ce za a ci gaba da tsare wani matashi da ake zargi da yin batanci ga manzon Allah, Yahaya Aminu Sharif, har sai an yi gyararraki a kan kararsa da aka yi a kotun shari’ar Musulunci.

Sannan alƙalin da ya saurari ƙarar ya ce rashin lauya mai tsaya wa Yahaya ya ci karo da dokar kare haƙƙin waɗanda aka tsare bisa ko wane laifi kuma dole ne kotu ta tabbatar da samar masa lauya.

Yahaya Aminu Sharif: Kotun Daukaka Ƙara ta ce a koma kotun Musulunci Wanda Yayi Ɓatacin Ga Manzon Allah (S.a.w)

Sai dai alkalin ya bayar da umarnin cewa wani alkali na daban ne zai sake sauraron shari’ar Yahaya Aminu a kotun musuluncin, wato ba wanda ya saurari karar da farko ba.

Don haka yanzu za a yi sabon zaman sararen karar Yahaya Aminu Sharif ne a kotun Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey a jihar Kano.

A watan Satumbar 2020 ne Yahaya Aminu Sharif ya daukaka kara bayan Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin a wata waka da ya yi a shekarar 2019.

Matashin, mai shekara 22 dan asalin birnin Kano, ya musata zargin da aka yi masa na yin batanci ga manzon Allah.

Sai dai kotun ta ba shi damar daukaka kara.

Ko da kotun ta tabbatar da hukuncin kisan, dole sai gwamnan jihar Kano ya sanya hannu kafin a aiwatar da hukuncin a kan Aminu Yahaya Sharif.

Wata Sabuwa ! Malam Ali Na Kwana Casa’in Yayiwa Malamin nan marar Tsoro Bin Kasim Martani akan Sakin Aure a Fim

Amma gwamnan jihar Kano a Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan takardar hukuncin idan ta isa hannunsa.

Haka kuma, kotun ta kori hukuncin babbar kotun Musulunci da a farko ta kama Umar Faruk da laifin ta kuma aike da shi gidan gyara hali tsawon shekara 10.

Kamar yadda BBCHAUSA Kotun Daukaka karar ta ce dalilinta na korar karar shi ne a lokacin da ya aikata laifin shekarunsa ba su kai 18 ba don haka ta ce a saki Faruk Umar.

Wane ne Yahaya Sharif-Aminu?
An haifi Yahaya Sharif-Aminu a unguwar Sharifai, a gidan Mallam Aminu Sha’aibu Sharifai wanda malamin addini ne kuma mai yabon Manzon Allah SAW.

Ya fara karatu a makarantar firamaren ‘yan awaki da ke unguwar Koki, sannan ya wuce karamar sakandire a GATC Gwale daga aji 1 zuwa 3.

Bayan ya kammala sakandire ne sai ya bar karatu ya koma sana’ar saye da sayarwa ta takalma.

Haka kuma ya yi karatun addinin Islama a gaban mahaifinsa, wanda ya yi da’awa a jawabin da ya gabatar a gaban kotu na cewar mahaifin nasa shi ne shehinsa.

Ya ce shi dan kungiyar Faira ne a darikar Tijjaniya kuma yana gabatar da salloli biyar a kullum.

Ya hada wani dandali na Whatsapp da ya yi wa lakabi da Umma Abiha, wato dandalin masoya ‘yar manzon Allah SAW.

A ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu, 2020, a lokacin da suke hirar addini a dandalin aka sami wani ya soki darikar Tijjaniya yana mai zargin suna tafiya daidai a inda shi kuma ya nadi muryarsa ta (Voice be aware) inda ake zargi ya yi kalaman batanci ga Manzan Allah SAW, wanda ya yi su ne saboda an soki darikar Tijjaniya da yake bi.

Bayan yin kalaman nasa ne sai ya sayar da wayarsa ya yi kudin mota zuwa Jigawa domin gudun abin da zai je ya dawo.

- Advertisement -