Yadda Zazzau Da Zazzagawa Suka Karbi Sabon Sarkinsu

0
122

Tun daga ranar Laraba bakwai ga watan Satumba shekara ta 2020 da gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sunan Magajin garin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na goma sha tara , wanda ya fito daga gidan Mallawa a cikin gidajen sarauta hudu da sukemasarautar Zazzau, duk inda ka za ga a birnin Zariya musamman manyan hanyoyi da suka hada da Kofar Doka zuwa cikin birnin Zariya da Babban Dodo zuwa fadar Zazzau da dai sauran hanyoyi, babu abin da idon ka zai nuna maka sai jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro na farin kaya.

Binciken da wakilinmu a Zariya ya gudanar ya gano cewar, gwamnati ta sa jami’an tsaron ne domia sa idon tabbatar da tsaro bayan ta bayyana sabon sarki da aka kwashe kwana goma sha bakwai, gwamnatin jihar ba ta bayyana wanda za ta nada ba ya gaji marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris. Wannan samun dogon lokaci da gwamnati ba ta bayyana sabon Sarkin ba, ya zama silar bayyana jita jita a kafafen watsa labarai na zamani, yau ka ji wane cikin ma su nema gwamnati ta ba shi takardar ya zama sabon Sarkin Zazzau na goma sha tara a masarautar Zazzau, jan kafar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, shi ma ya zama babban dalilin da ma su yada jita-jita suka dinga bayyana cewa gwamnatin ta watsar da wadanda masu zaben sarki su biyar, wato Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu da Fagachin Zazzau Alhaji Ummaru Mohammed da Makama Karami Alhaji Mohammed Abbas da babban Limamin Zazzau Alhaji Dalhat Kasim Ima da kuma Limami Kona na Zazzau Alhaji Muhammad Sani Aliyu suka zaba a cikin wadanda suka zama kan gaba wajen neman wannan kujera ta Sarautar Zazzau.

Yadda Zazzau Da Zazzagawa Suka Karbi Sabon Sarkinsu

Kwatsam a ranar Laraba da ta gabata sai gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da takardar bayyana Magajin Garin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau, wanda ya sa hannu a wannan takarda shi ne Kwamishinan kula da ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Kaduna Alhaji Jafaru Ibrahim Sani.
A wannan rana ta Larabar bayan gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kujerar karagar Zazzau ga Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, sai kuma al’umma suka fara bayyana a fadar Zazzau, domin yi wa sabon Sarki mubayi’a. Bayan an kwashe kimanin sa’o’i biyu sabon Sarkin Zazzau na karbar mubayi’a, sai kuma aka fito da motar da marigayi Sarkin Zazzau ke hawa, aka dauki sabon Sarkin zuwa gidansa, bisa rakiyar Sarkin Dogaran Zazzau da kuma motar jiniya.

A ranar Alhamis, kwana daya da gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kujerar karagar Zazzau ga Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, da safiyar wannan rana, duk wanda ke Zariya, ya ga jirgin sojoji na zaga saman birnin
Zariya zuwa Tudun Wada zuwa Sabon Gari.

Tsokacin da al’umma suka yi kan wannan jirgi shi ne, an sa jirgin ne ya yi yawo a sama, ko za a gano wasu matsaloli da za su taso a dalilin bayyana sabon sarkin Zazzau da gwamnatin jihar Kaduna ta yi. Har dai zuwa hada wannan rahoto, babu wasu matsalolin tashin tashi na da suka ta so a dalilin bayyana sabon sarkin, idan ma ka je kofar gidan sabon sarkin da ke Unguwar Kwarbai a birnin Zariya, tamkar ana cin kasuwa ne, wato raye-raye da kuma bushe-bushe da mawaka da makada ke yi. Wasu al’umma da wakilinmu ya zanta da su photo voltaic bayyana ra’ayoyinsu da wannan nadi da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, musamman na yadda gwamnatin ta dinga jan kafa.

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Shimfida Tsarin Gina Kasa A Madina Bayan Hijira

Alhaji Armaya’u Suleiman, Banagan Zazzau, wanda yake daya daga cikin manyan abokan tsohon sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris, ya bayyana cewar nadin da aka yi wa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, babu shakka, shi Allah ya kaddara zai zama sarki a Zazzau. Alhaji Amaya’u Suleiman ya shawarci sabon sarkin da ya rike mutane
bisa adalci da kuma amanar da za su zama abubuwan da za su ciyar da masarautar Zazzau da al’umma da kuma jihar Kaduna gaba, ya kuma yi kira ga al’ummar masarautar Zazzau kafatan da su ba sabon sarki duk
goyon bayan da suka dace. Domin ya sami saukin auke nauyin da gwamnatin jihar Kaduna ta dora ma sa.

Shi kuwa Alhaji Al’amin Suleiman, Turakin Lere, ya fara da cewar, babu ko shakka nada Jakada Ahmed Nuhu Bamalli sarkin Zazzau, abin farin ciki ne ga duk masoyin masarautar Zazzau da kuma jihar Kaduna baki daya, yana
mai cewar, a matayinsa na wanda ya san mulki ya kuma gaje ta. Ya san zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo ci gaba mai dorewa a masarautar Zazzau.
Shi ma Turakin Lere, ya yi kira ga al’ummar maarautar Zazzau su manta cewar wane da wane photo voltaic nemi sarautar, su tashi tsaye na ganin photo voltaic ba shi duk hadin kan da suka kamata, domin ci gaban masarautar Zazzau da jihar Kaduna baki daya.

A nashi bangaren, Alhaji Abubakar Lawal Atikuy, matashi mai tallafa wa al’umma a Zariya, da farko cewa ya yi baya ga farin ciki da al’ummar Zazzau ke yi wa sabon sarki, ya ce kamata yay i su tashi tsaye wajen yi ma sa addu’o’i dare da kuma rana, domin ya sami saukin fuskantar ayyukan da suka hau kan san a sabon sarkin Zazzau na goma shara tara. Alhaji Abubakar ya kuma shawarci sabon sarkin da ya rungumi kowa da kowa, musamman ya lura da gidajen sarauta da suke maarautar Zazzau, da suka hada da Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Sullubawa da kuma Gidan Katsinawa, ta haka, a cewarsa, sai ya sami saukin fukantar nauyin da Allah ya dora masa.

What's On Your Mind?