Yadda Za A Kawo Karshen Ta’addanci A Arewa Maso Yamma — Gwamna Ganduje

0
140

Yadda Za A Kawo Karshen Ta’addanci A Arewa Maso Yamma — Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba da shawarar gudanar da ayyukan ‘yan sanda, inganta kudade da samar da kayayyakin aiki ga hukumomin tsaro, da tura fasahar zamani a matsayin hanyar magance saurin hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

Ganduje, wanda ya bayar da wannan shawarar a Katsina, lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, don yi masa ta’aziyya a kan rikicin gobarar da ta faru kwanan baya inda ya tabbatar da cewa aikin ‘yan sanda na gari zai samar da kyakkyawan yanayi da goyon baya wajen samun nasara a yakin da ake yi da ’yan ta’adda a yankin.

Sukar Buhari: Karon Farko Hadimin Ganduje Ya Magantu Bayan Dakatar Da Shi

Yayin da yake yabawa wasu abokan aikin sa a yankin, wadanda suka dauki matakan tsaro da dama domin magance ‘yan bindiga a jihohin su, ya shawarci wadanda har yanzu basu yi hakan ba da su dauki aikin ‘yan sanda na gari da kuma amfani da fasaha.

A nasa bangaren, Masari ya godewa Ganduje da mukarrabansa bisa ziyarar, lura da cewa babu wani babban banbanci tsakanin jihohin biyu.

Ya ce, “Mun raba kan iyakokinmu mafi tsawo, kuma dangantakar da ke tsakaninmu ta kasance shekaru. Ba na ganin iyakoki da bambance-bambance amma dacewar mulki.”

What's On Your Mind?