Yaki Da Rashawa: Yadda Wasu Jami’an Tsaro Ke Kawo Cikas A Nijeriya 

0
56

Daya daga cikin sakandamin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tutiya da shi, shi ne daura damarar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nijeriya. Haka kuma, matsalar rashwa babbar annoba ce wadda ke yiwa duniya barazana tare da kawo cikas ga ci gaban diyaucin kasashen a duniya.

Bugu da kari, yaki da wannan mummunar halayya ta rashawa jan aiki ne wanda sai an taru hadi da cikakken shiri, musamman a kasashen Afrika a kebance kuma ga irin Nijeriya, inda girman matsalar ya zarta ma’aunin da wasu kasashen da ba ita ba. Wanda bisa yadda al’amarin ya yi zurfi, cin hanci da karbar rashawa ya na neman zama alakakai da kokarin zama wani bangaren rayuwar al’umma.

Yadda Wasu Jami’an Tsaro Ke Kawo Cikas A Nijeriya 

A tarihi da yanayin wannan alkaba’i, a zamanin dauri can ma ya rusa manyan dauloli ma su karfin tattalin arziki da fada a ji a duniya. Haka kuma, munin karbar rashawa da bayar da ita babbar ja’ifa ce ga mutane gama-gari, balle a tsakanin mahukunta ko uwa uba masu tsaron kasa- wanda idan hakan ta faru, sai dai a shafa fatiha a tashi.

Ko shakka babu, gwamnatoci su na iya nasu kokari a salon yaki da bazuwar wannan annobar, amma abin al’ajabi, abin kullum sai dada bazuwa yake tamkar gobarar daji, da tafiya irin ta bakin maciji a duhun dare- wanda sai cikakken shirin taron kwararru ne kadai zai bayar da nasarar yakar sa.

Gefe guda kuma, a halin da ake ciki, da jimawa yan Nijeriya ke bayyana korafe-korafen yadda wannan tabargaza ta rashawa ta kunno kai a tsakanin jami’an tsaron kasar nan, wanda a wasa-wasa, dukan mai bin manyan hanyoyin kasar nan ganau ne dangane da wadancan zarge-zargen da ake yi wa wasu jami’an tsaron da ke kula da shingayen ababen hawa da makamantan su.

Saboda muhimmancin aikin tsaro ga kasa, ya dace gwamnatin tarayya ta dubi wadannan koke-koken don ceto kasar nan daga sukurkucewar kyakkyawar alakar da ke tsakanin jami’an tsaro da jama’a, a shingayen binciken ababen hawa da ofisoshin yan-sanda da makamantan su a fadin kasar nan. Sau tari muryoyin jama’a na tashi cike da zarge-zargen karbar na goro a wurare daban-daban, wanda kuma ko shakka babu akwai bukatar gwamnati hadi da wadanda nauyin hakan ya rataya bisa ga wuyan su, wajen bincikar zargin tare da daukar kwakkwaran matakai.

Bidiyo: Mutumin da Ba Ya Tsoronsa Ya Ce Karya Ne Babu Boko Haram Sai Cinikin Boko

Ba wani abu babe boyayye, ga duk mai bin manya da kananan hanyoyin kasar nan, dangane da yadda su ka yi kaurin suna wajen karbar na goro ga direbobi da matafiya, wanda bisa hakikanin gaskiya wannan babban koma-baya ne ga ikirarin gwamnatin tarayya na yaki da rashawa. Haka kuma, barazana ce ga halin da a ke ciki na cigaba da fuskantar matsalolin tsaro.

A hannu guda, wannan matsala ce wadda za ta kawo koma baya a yakin da gwamnati ke kokarin yi a fannin rashawa da ta tabarbarewar tsaro a kasa. Sannan kuma babbar barazana ga tagomashi tare da kwarjinin da jami’an tsaron kasar nan ke da shi a idon yan kasa kana zai jawo kallon hadarin kaji, tsana da tarzoma wani lokaci. Hakan zai samar da babban gibi ga amincewar da ’yan kasa ke bai wa jami’an tsaro wanda hakan nakasu ne.

Ga duk mai bibiyar hanyoyin mota a fadin tarayya Nijeriya, ganau ne kuma bisa ga yadda labarai ke kai komo, an sha samun tarzomar da ke kai ga rasa rayuka, tsakanin direbobi ko kungiyoyin su da jami’an tsaro a wadannan wurare, al’amarin da ya dace kawowa yanzu gwamnatin tarayya ta dauki matakan shawo kan wannan matsala.

Har wa yau, duk da ba a taru a ka zama daya ba, amma wannan matsala ta karbar na goron, kusan ta hada kowane bangaren jami’an tsaro a kasar nan (masu sanya kaki)- face wasu kadan daga cikin jami’an tsaron. Wanda su ma masu irin wannan halin ya dace su gyara kuma su kula da manar da aka damka musu ta kare kasa da yan kasa tare da dukiyoyin su.

Ya dace gwamnati ta kalli wannan lamari da tabaraun hangen nesa don gano hakikanin abinda ke wakana: shin daga ina ne wannan matsala take- ta fuskar manyan ne ko kurata ne? Ko kuma matsalar albashi da alawus din jami’an tsaron ne ba ya isa, ko wata matsala ce ta daban? Wata zolayar da kowa ke mamaki a kanta dangane da wadannan shingayen binciken ababen hawa, shi ne kafin ka je daf da jami’in tsaron da ke aikin binciken ababen hawan, za ka ga an rubuta a allon sanarwa cewa: “Kuskure ne bayar da cin hanci ko karbar sa a wannan waje”. Amma ka na isa wajen gogan naka zai zuro maka hannu tare da nuna maka cewa ka bashi na shan ruwa!

Da zarar direba ya noke ko ya fahimci da bakuwar fuska a motar, nan take zai umurci direban da cewa, “Hey driber come proper right here, park there”: Kai direba zo nan, je can ka tsaya. Ya na muzurai, dole sai an biya sannan a wuce. Haka kuma, idan kayan abinci ko na sha ka dauko, a nan za su yi ta murza maka gashin baki har sai ka mika musu nasu kason, hatta motar itace ba su bari ba- ba su damu duk abinda zai faru ba, balle fargabar me ka zo dashi.

An sha yin tata-burza da ja-in-ja tsakanin bangarorin biyu, wanda ko shakka babu, hakan tamkar tozarta aikin tsaro ne. Ya dace gwamnati ta sake kallon wannan muhimmin bangare tare da sake farfado dashi daga hannun maras kishin kasa, saboda babu aiki mai kima da daraja ga dorewar martaba da diyaucin kasa kamar tsaro, sannan barin sa haka kara-zube babbar barazana ce kuma tamkar wasa da rayuwar yan kasa ce.

Jami’an tsaro da aikin tsaron kasa babban al’amari ne wanda ya dace gwamnati, yan kasa da su kansu jami’an tsaron ya dace su bashi mashahurin muhimmanci. Duk kasar da ta kasa kare tsaron ciki da wajen kasar ta, to ko shakka babu an ga wallenta kuma ba tada sauran katabus- kawaye da takwarorinta za su rika yi ma ta kallon huhun ma’ahu.
Sannan ita kuma rashwa tamkar bakar annoba ce, za ta ruguza komai da kowa a duk lokacin da ta saka gabanta.

What's On Your Mind?