Yadda Ta Kaya A Zaben kananan Hukumomin Jihar Bauchi

0
67

Yadda Ta Kaya A Zaben kananan Hukumomin Jihar Bauchi

A jiya Asabar ne hukumar zabe ta jihar Bauchi ta ware domin gudanar da zaben shugabanin kananan hukumomin jihar su 20 da kuma Kansiloli 323 da suke fadin jihar. Inda aka fafata neman sa’a a tsakanin jam’iyyun siyasa guda 18 yayin da kuma zancen ya fi karamari a tsakanin APC da PDP mai mulkin jihar.

Jihar Bauchi dai ta shafe shekaru 12 ba tare da gudanar da zaben kananan hukumomi ba, illa dai tana amfani da kantomomin riko, sai a wannan karon ne aka samu zarafin aiwatar da zaben don baiwa kananan hukumomi ‘yancin cin kashin kansu musamman ta fuskacin aiwatar da aiyukan raya yankuna.

Tun wajajen karfe bakwai na safiyar jiyan manema labarai da masu sanya ido kan zabe suka fantsama lunguna da sakona na jihar domin gano da nakalto wa jama’a irin wainar da ake toyawa a fadin jihar kan wannan zaben na shugabanin kananan hukumomin.

Binciken da wakilinmu ya tabbatar shine an samu karancin isan kayayyakin gudanar da zaben a kan lokaci inda jama’a da dama suka yi korafin rashin zuwan kayan zaben a kan lokaci, wurare da daman gaske kayan zaben photo voltaic je a mare matuka, lamarin da ya sanya wasu da dama fusata da fasa yin zaben da suka shirya yi.

Duk da hakan dai wasu photo voltaic yi tsayuwar daka kana photo voltaic jira domin dangwala kuri’a don zabin wanda suke son ya shugabance su.

Sai dai malaman zaben photo voltaic nuna cewa mafiya akasari an samu tsaikon ne a sakamakon dabara da suka yin a fara kai kayan gudanar da zaben zuwa rumfuna da suke nesa a maimakon farawa da cikin gari. Ukasha Abubakar daya ne daga cikin jami’an gudanar da zaben a karamar hukumar Alkaleri, ya shaida ma ‘yan jarida cewa photo voltaic fara rabar da kayan zaben ga wurare masu nisa wannan dalilin ne ya janyo ba su fara aiwatar da zaben a kan lokaci ba. Sai dai jam’iyyar APC dai ta yi korafin cewa akwai shirin magudi da jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta kitsa wajen ganin ‘yan takaran APC ba su kai ga samun nasara ba.

Shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Darazo, Adamu Mohammed Maichibi, ya ce hatta rashin kai kayan zaben a kan lokaci wani shiri ne na magudi. Sai dai wani jigo a jam’iyyar PDP Nasiru Darazo ya karyata batun da cewa PDP na tafiya kan demokradiyya ne don haka za su baiwa jama’a damar su zabi abun da suke so ba tare da tursasawa ba.

Da ya ke jawabi bayan ya kada kuri’arsa, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya nuna jin dadinsa da farin cikinsa bisa yadda zaben yake tafiya ba tare da tashin hankali ko wani fitina ba, yana mai cewa jama’a suna da cikakken ikon yin zabin da suke so na shugabanni. Ya dai nuna cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta ci gaba da wanzar da ababen additional rayuwa da suka dace wa al’umma don haka ne ya sake neman hadin kan jama’a domin cigaba da kyautata jihar.

NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi Mai Nauyin Kilogram 2412.39 A Jihar Oyo

Ya jinjina wa jama’a a bisa gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da salama. Gwamnan wanda ya jefa kuri’arsa a mazabarsa da ke kauyen Duguri tare da kariyar matarsa Hajiya Aisha Bala Muhammad ya kuma jinjina wa jami’an gudanar da zaben a bisa nuna kwarewa wajen aikinsu. Ya ce, a shirye suke su tabbatar hukumar zabe ta jihar na kwaikwayon hukumar INEC wajen tabbatar da yin nagartacce kuma ingantacce zabe a kowani lokaci domin kyautata mulkin demokradiyya. Da ya juya kan batun da ya shafi kasa kuwa musamman kan matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankuna, ya nemi ‘yan jarida da su kasance masu kokarin hada kan Nijeriya ba masu farraka ‘yan kasa ba.

Dangane da masu zanga-zangar neman a rufe sashin ‘yan sanda na SARS gwamnan ya ce duk da akwai kurakurai kan wasu aiyukan ‘yan sanda amma fa suna da matukar amfani ga kasa, inda ya ce jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomi tsaro irin su soji, kwastam, jami’an kula da shige da fice da sauransu a matsayin wadanda suka sadaukar domin tabbatuwar Nijeriya a matsayin kasa daya don haka ne ya ce gyara ake bukata a wuraren da ake da matsala domin kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Ya dai hakikance da nuna muhimmancin jami’an tsaro a cikin al’umma, sai ya nemi da a kawo gyara cikin lamuran da za su kai ga tabbatar da kowa na cin moriyar ‘yancinsa na rayuwa a cikin kasar nan.

Wakilinmu ya shaido cewa har zuwa lokacin da yake aiko mana da wannan rahoton hukumar zabe ba ta ayyana sunayen wadanda suka lashe zaben ba, sai dai wasu yankuna da dama photo voltaic kamamala gudanar da zabensu ya zuwa lokacin da muke kammala aiki kan wannan rahoton.

What's On Your Mind?