Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

0
67
  • Mazauna wasu unguwanni na fama da korafi a kan sace-sacen garin tuwo da ake masu a wajen nika a birnin Kano

  • Faruwar wannan al’amari ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika

  •  Sai dai an danganta wannan lamari da halin da talaka ya tsinci kansa a ciki na matsayin rayuwa da tsadar kayan masarufi

A yayinda talakawa ke ci gaba da kukan babu da matsin rayuwa, mazauna wasu unguwanni a birnin Kano, na korafi a kan yadda ake sace masu garin tuwonsu a wajen nika a yan kwanakin nan.

A lokutan baya da wuya ka ji an ce an sace garin tuwo a wurin nika sai dai a samu yanayin da ake yin musaya bisa kuskure, wato wani ya dauki na wani.

An tattaro cewa wannan sabon sauyi da aka samu na sace-sacen garin ya sanya wasu masu injin nika solar fara ba da katin shaida domin rage afkuwar hakan.

A yanzu idan mutum ya kai nika, sai a bashi katin shaidar cewa ya kai nika wajen.

Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce an samu karin mutum fiye da miliyan guda da ke fama da karancin abinci a jihar Kano sakamakon annobar korona, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sai dai kuma, mutane da dama na danganta al’amarin da irin matsin rayuwar da jama’a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi.

An dai samu tashin farashin kayayyaki sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi.

A wani labarin, kimanin iyalai 12,100 da kuma masu kananan sana’o’i na jihar Kano zasu amfana da tallafin COVID-19 a jihar, a cewar wakilin UNDP Muhammad Yahaya.

Kamar yadda wakilin UNDP, Muhammad Yahaya ya bayyana, an bada wannan tallafin ne don taimakon ‘yan jihar.

What's On Your Mind?