Yadda Sallar Idin Wannan Shekarar Ya Gudana A Legas

- Advertisement -

Yadda Sallar Idin Wannan Shekarar Ya Gudana A Legas

Daga Bala Kukkuru,

Dubban dubatar al’ummar musulmin Nijeriya da duniya baki daya ne suka kammala ibadojin su na a azumin watan Ramadan na bana a cikin wannan shekarar aranar Alhamis din nan information gabata kuma suka yi idi aranar jumma’ar information gabata tare da gudanar da adduo’i na musaman ga kasa domin kara neman izini a wajan Allah ubangiji subahanahu wata ala na cigaba zaunar da kasar Nijeriya lafiya baki daya kamar yadda malamai magada annabawa da sauran al’umma suke gudanar da irin wannan adduoi.

Malam Imam Suleman Ibrahim babban limamin masallacin jumma’a, anan tsibirin rukunin gidajen unguwar Wantauzan an o biktoriya ailan Legas kuma shugaban izala reshen jihar Legas yana daya daga cikin malamai masu gudanar da irin wadannan adduoi kuma shi ne ya jagoranci sallar idin a masallacin Jumma’ar da ke unguwar wantauzan an fo inda a cikin hudubarsa ta sallar idin ya cigaba da jawo hankulan malamai da sauran al’ummar kasar nan dasu cigaba da gudanar da Irin wadannan adduoi tareda sanya mabiyansu bisa kan hanyar akidar zaman lafiya haka zalika ya kara da cewa suma sauran al’umma suna da tasu gudummawar ta rawar da za su taka a wajen kawo zaman lafiya baki daya

Sheikh Suleman Ibrahim da ya ke tsokaci abisa kan matsalolin tsaro a kasar nan kuwa cewa ya yi maganar matsalar tsaro a Nijeriya ba Gwamnati ba kawai za ta lura da al’amarin suma Jama,ar gari suna da tasu rawar da za su taka a wajan kawo karshen matsalar tsaro a kasar san nan kuma ya cigaba da shawartar al’umma dasu cigaba da bai wa Jamian tsaro hadin kai da goyan baya a wajen basu dukkan wani sirri ko wadansu mutane gane masu ba domin kawo karshen duk, kan miyagun ayyaka da ta’addanci wanda yake faruwa a kasar nan baki daya.

Sannan kuma ya cigaba da shawartar Gwamnati information kara yin shiri na musamman a wajen samar wa matasa ayyukan yi domin kaucewa faruwar irin wadannan miyagun ayyaka da ta’addaci a kasar nan baki daya ya kara da cewar harkar matsalar tsaro a halin yanzu na ta kowa da kowa ce bawai sai Gwamnati ba ko kuma wa dansu mutane da bam ba yace sabo da haka kowa da kowa yafito domin tabbatar da tsaro a kasar nan domin kowa ya samu sukuni na zirga zirga da sauran al amuran da suka shafi rayuwar al’umma gaba daya in jishi da fatan Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da kasar mu Nijeriya lafiya baki daya.

San nan kuma ya cigaba da shawar tar Gwam natin Taraiya information kir kiro wadan su wurare na koyama al’umma da sauran matasa sanaoln hannu domin ita kanta Gwam natin ta samu sauki awajan nemar ma al’umma wuraren aikin dogaro da kai san nan kuma ta kara Ingan ta makarantun boko dana arabik domin Jama, a su samu Ilimin da zai nuna masu aiki mai kyau da aiki mara kyau acewarshi da fatan Gwam natin za ta dauki wan nan shawara tashi baki daya.

karshe yace yana yima duk kan al’ummar musulmi fatan alheri na kammala a zumin Ramadan na lafiya in jishi da fatan Allah ubangiji ya sanya Ibadojin duk kan musulmi kar babba ce ya kuma cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya da sauran kasashen musulmi baki daya.

 

- Advertisement -