Yadda NIS Ta Tantance Sabbin Jami’an Da Aka ɗauka Su 4,120 – Babandede

- Advertisement -

Yadda NIS Ta Tantance Sabbin Jami’an Da Aka ɗauka Su 4,120 – Babandede

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) CGI Muhammad Babandede ya sake gargaɗin cewa duk wani jami’i da aka kama da hannu wurin karɓar cin hanci da rashawa da sunan samar wa wani aiki ko domin wani aiki na daban a hukumar zai ɗanɗana kuɗarsa.
Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a kan sabbin jami’an da NIS ta ɗauka daga cikin waɗanda suka nemi aiki da ita wajen sama da mutum 500,000.
Babandede ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi wata-wata wurin maganin duk wani mai kunnen ƙashi da aka kama yana tatsar ‘Yan Nijeriya kuɗi da nufin samar musu guraben ayyuka a hukumar ba.
Ya ce a ƙoƙarin da hukumar take yi na tsaftace ayyukanta da kawar da bara-gurbin jami’ai, ko a kwanan nan solar tasa ƙeyar wani jami’i da wani takwaransa na hukumar gidajen gyaran hali zuwa Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ICPC domin tuhumarsu da damfarar wasu ‘Yan Nijeriya da ba su ji ba ba su ga ba, wajen Naira Miliyan 15 da nufin samar musu aiki da NIS.
Shugaban ya kuma yi kira ga ‘Yan Nijeriya su kai rahoton duk wani jami’i da ya nemi kuɗi a hannunsu ko wanda ya riga ya karɓi kuɗin ko da ya kai tsawon shekara da faruwar hakan, inda ya sha alwashin cewa za su ƙwato wa mutum haƙƙinsa, “ko da kana cikin waɗanda suka samu nasarar shiga jerin waɗanda za a ɗauka a cikin wannan sabon zubin kar ka ce tun da ka samu ka bar masu kuɗin, a’a, ka kawo rahotonsu za mu bi maka haƙƙinka. Aikin NIS kyauta ne, ba a karɓar ko kobo. Kuma duk wanda muka kama yana karɓar wani abu daga hannun al’umma za mu tabbatar da cewa an hukunta shi bisa doka”.
Wakazalika, Babandede ya ce mutanen da suke fakewa da aikin NIS suna damfara na ƙara ɓullo da sabbin dabaru kullum ciki har da amfani da sunansa a wurare daban-daban domin karɓar kuɗi ko kuma buɗe shafukan sada zumunta da hotunansa, “to duk waɗannan ƙarya suke yi, ‘yan damfara ne, kowa ya yi hankali da su. Akwai wani ma da ya tafi Jigawa wajen wani ciyaman ya ce ya ba shi kuɗi da sunana. Allah ya sa ciyaman ɗin yana da lambata sai ya kira ni, na ce masa ban aiki kowa ba, Allah ya sa akwai jami’anmu (na NIS) a kusa sai suka kama mutumin suka damƙa shi ga ‘yan sanda. Na kira kwamishinan ‘yan sanda na faɗa masa cewa a tabbatar an hukunta mutumin nan. To haka suke yi, kuma ba za mu bar su ba za mu ci gaba da bincike mu bankaɗo su domin hukunta su”, in ji shi.
Hukumar ta bayar da kafofin da za a kira a kai rahoto ko ƙorafi sport da ɗaukar aikin ko wani al’amari na cin hanci da rashawa da suka haɗa da lambar waya 08033000487 ko shafin intanet na hukumar [email protected], ko kuma a kai rahoton abin ga Humar ICPC ko takwarorinta da ke yaƙi da cin hanci da rashawa.
Da yake jawabi sport da ɗaukar sabbin jami’an, CGI Muhammad Babandede ya yi bayanin cewa bayan tantancewa a matakai daban-daban, hukumar ta fitar da sunayen mutum four,120 waɗanda suka samu nasara da za su hallara a cibiyoyi daban-daban domin gudanar da jarrabawar ƙarshe. Ya ce za a buɗe shafin da kowa a cikin waɗanda suka tsallaka za su shiga domin duba sunayensu da kuma fitar da ‘yar takardar da take ƙunshe da bayani da cibiyar da kowa zai je ya rubuta jarrabawar.

Babandede ya ƙara da cewa, “daga cikin mutum 500,000 da suka nema a farko, mutum 334,554 ne suka yi nasarar cike abubuwan da ake buƙata. Daga cikin wannan adadin, an tantance waɗanda suka dace su 75,155, daga cikinsu aka sake tantance 45,323, sannan har ila yau aka gayyaci mutum 6,105 domin tantance takardun karatunsu da yanayin ƙoshin lafiyarsu. Daga cikinsu ne kuma aka fitar da jerin sunaye na ƙarshe na waɗanda za a ɗauka su four,120 bisa amincewar gwamnati” kamar yadda ya bayyana ta hotunan majigi.
Wakazalika, shugaban hukumar ya bayyana jihohi da aka haɗe su a shiyyoyi wadda waɗanda ka ɗaukan za su hallara domin tantancewar ƙarshe, inda ya ce waɗanda suka fito daga shiyyar arewa maso gabas da suka ƙunshi Jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe za su je Bauchi. ‘Yan jihohin arewa ta yamma da suka ƙunshi Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sakkwato da Zamfara kuma za su je Kano. Sai ‘yan yankin kudu maso kudu da suka haɗa da Jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Kuros Ribas, Delta, Edo da Ribas kuma za su je Ahoda, kana ‘yan yankin kudu maso gabas da suka ƙunshi jihohin Abiya, Anambara, Ebonyi, Enugu da Imo da za su Onu domin tantancewar. Su kuwa waɗanda suka fito daga yankin arewa maso tsakiya da suka ƙunshi Benuwai, Abuja, Kwara, Nasarawa da Neja za su tafi Minna, sannan ‘yan yankin kudu maso yamma da suka haɗa da jihohin Legas, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti za su je Legas domin tantancewar ta ƙarshe.
Tun da farko da take jawabi, Darakta kuma Babbar Sakatariyar Hukumar Gudanarwar Hukumomin Shige da Fice, Gyaran Hali, Kashe Gobara da Rundunar Tsaron Fararen Hula, Hajiya Aisha Rufai ta bayyana cewa an bi dukkan ƙa’idojin da suka kamata wajen ɗaukar sabbin jami’an na NIS.
A cewarta, an bi ƙa’ida tun daga matakin farko na gabatar da buƙatar ɗaukar sabbin jami’an ga shugaban ƙasa tare da jiran amincewarsa har zuwa tantance sabbin jami’an ta fuskar kima da mutunci da gwajin shan ƙwayoyi da tallata lamarin a jaridu da sauran ƙa’idoji na raba-dai-dai a tsarin tarayya da ake amfani da shi a ƙasar nan.
Ita ma ta gargaɗi ‘yan cuwa-cuwa su yi wa kansu ƙiyamullaili su daina damfarar ‘yan ƙasa da nufin samar musu da aiki, inda ta ce gwamnati tana ankare da irinsu kuma duk wanda aka kama zai kwashi kashinsa a hannu.
Haka nan ta gargaɗi sabbin jami’an da za a ɗauka cewa kar kowa ya tafi cibiyoyin da aka tura su da ‘yan rakiya, kowa ya je shi kaɗai, sannan duk wanda bai je a lokacin da aka tsara ba zai rasa.
Daga ƙarshen taron dai an gabatar wa da ‘yan jarida sabbin manyan mataimakan kwanturola janar guda biyar da shugaban ƙasa ya amince da ƙara musu girma da suka haɗa DCG Haliru, DCG Yerima, DCG Wunti, DCG Ade-Poju da kuma DCG Opara.
……….
Babbar Sakatariyar Hukumar Gudanarwar Hukumomin Shige da Fice, Gyaran Hali, Kashe Gobara da Rundunar Tsaron Fararen Hula, Hajiya Aisha Rufai (ta huƙu a dama), Shugaban NIS, Muhammad Babandede (na biyar a dama), Babban Mataimakinsa DCG Isah Idris Jere (na uku a dama), sauran manyan mataimakansa da aka ƙara musu girma; DCG Ade-Pouju (a dama), DCG Wunti (na biyu a dama), DCG Haliru (na uku a hagu) DCG Yerima (na biyu a hagu) da DCG Opara (a hagu), bayan kammala taron manema labarai a shalkwatar NIS ranar Juma’a

 

- Advertisement -