Yadda Nake Hada Ba Da Maganin Gargajiya Da Aikina Na Dan Sanda – Malam Ibrahim

0
71

Yadda Nake Hada Ba Da Maganin Gargajiya Da Aikina Na Dan Sanda – Malam Ibrahim

Wakilinmu da ke Zariya ISA ABDULLAHI GIDAN bAKKO, ya sami damar tattaunawa da fitaccen mai bayar da maganin gargajiyar nan da ke zaune a garin Kaduna wanda aka fi sani da MALAM IBRAHIM Baiwa daga Allah, wanda har ila yau, a halin yanzu, wannan bawan Allah jami’ai ne na hukumar ‘‘yan sanda ta kasa a garin na Kaduna, inda ya amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa musamman kan yadda yake aikin dan sanda da kuma tallafa wa masu lalurar kwakwalwa da jinnu da sauran matsaloli rashin lafiya da suke addabar al’umma.

Ga yadda tattauwar ta kasance.

Da farko masu karatu za su so jin cikakken tarihin rayuwarka
To ni dai an haife ni a garin Gusau da ke Jihar Zamfara, kamar kowane yaro a Arewacin Nijeriya, tun ya na karami iyayensa su kan sa shi a makarantar Allo, amma ni mafiya yawan karatun addini da Allah ya ba ni ikon yi, a gaban mahaifi na na yi,

Kuma na sami damar yin karatun zamani tun daga firamare ya zuwa gaba da sakandare a garin Gusau, bayan karatun da na yi ne, sai na sami damar shiga aikin dan sanda, wanda har lokacin zantawar nan da mu ke yi, ni cikakken dan sanda ne a nan garin Kaduna.

To yaushe ka shiga aikin dan sanda ?
Na shiga aikin dan sanda a 2001,

Me ya ja ra’ayinka zuwa aikin dan sanda ?
Eh to a gaskiya na shiga aikin dan sanda ne domin ina son aikin tun ina karami, kuma kamar yadda wasu ke kallon ‘‘yan sanda da a matsayin mutane marasa kirki ba su da imani da dai sauran batutuwa marasa kyau ni da Allah ya san a shiga wannan aiki a duk rana kara imani da tausayi da hakuri da hangen nesa da kuma fauwala wa Allah nake kara samu. Har ila yau na yi karo da wa’azi da yawa da karin tsoron Allah, a wasu lokuta ma sai in ga kamar lahira ce ke kusanto ni.

Ko zaka iya ba mu misalin wasu abubuwan da ba za ka manta da su ba daga shigarka wannan aiki zuwa yau?
A wasu lokuta zan yi ido biyu da abokin aiki na da aka ce azzalumai ne, bayan an je sai ka ga an dawo da dan uwana a aiki, ba da rai ba, wannan na daga cikin wa’azin da na ke dauka a kullum cewar za ta iya faruwa da ni, kuma wannan na kara sa in ji tsoron Allah a duk inda na tsinci kaina a wannan aiki na dan sanda.
Ko kuma wannan mutum na san shi kila shugabana ne, sai ka ga ya sami rashin lafiya, sai ka ga bai iya tashi bai kuma iya magana ballantana ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa, sai in tuna a lokacin da yake da rai, dare da rana muna tare a wajen aiki da sauran huldodi, yana ba mu umarni, amma yau ga shi komai sai an yi ma sa, wannan na kara min imani da tausayin duk wanda na yi hulda da shi, musamman a wannan.
Kuma a duk lokacin da aka ce ga hadari ya faru, sai in yi tozali da mutum dan uwa da kafin hadarin ya iya tafiya yana iya magana, ya kuma tashi ya yi magana, amma wannan hadari ya sa babu ko da daya da da zai iya yi, wannan na kara sa mani imani a cikin wannan aiki.

A bangaren mutanen kuma, sai ka ga mutum a ido cikakken mutum, amma in an fara gudanar da bincike kan matsalolin da suka sa aka kai shi ga ofishin ‘‘yan sanda, sai ka ga mutumin azzalumi ne, musamman ya cutar da mutum ko kuma mutane ba tare da tsoron wanda ya halicce shi ba, wasu ma har marayu suke cuta, kamar wata matsala da na taba gani ta wasu da aka cuce su, su ka kai gabanmu, ni da kai na, sai da na zubar da hawaye sanadin cutar da aka yi wa wadannan marayu.
A mafiya yawan lokuta in na ga ire-iren wadannan matsaloli, da farko sai na yi wa wanda ya yi cutar wa’azin ya sa tsoron Allah a zuciyarsa, daga nan sai ka ga na fara samun damar da zan warware wannan matsala da aka gabatar gabana na dan sanda mai bincike.

Ka taba tsintar kanka a ganin ya dace ka bar wannan aiki na dan sanda ?
Kamar yadda na bayyana maka a baya, imanin da ke shigo ni shi ya ke yi mani jagora na ayyukan dan sanda da kuma sauran ayyukan tallafa wa al’umma da na ke yi dare da rana, amma ban taba tunanin na bar wannan aiki a dalilin wani ko kuma wasu abubuwa da na gani ba, in na wayi gari na bar wannan aiki, sai dai domin zuciyata ce ta nuna min in bar wannan aiki na dan sanda, kuma har zuwa tattaunawar da mu ke yi, babu wannan tunani a cikin zuciya ta dai-dai da rana guda.

Ya ka tsinci kanka a wannan hanya ta tallafa wa al’umma da maganin wasu cutttuka da suke addabarsu ?
A gaskiya ita daukaka ta Allah ce, amma ina tabbatar maka cewar, wannan baiwa daga cikin jikina take tun ina yaro, iyayena da kuma wadanda na taso tare da su solar san haka, tun daga haduwa da wasu mutane na fara fadada wannan baiwa da Allah ya ba ni, ta ba su maganin wata cuta da ta ke addabarsu, da kuma yin tsayin daka ga ko wace irin matsala da ta zo gaba.
Baiwar da Allah ya ba ni ko wace irin cuta da dan’Adam ke fama da ita, da zarar ya gurfana gareni, cikin ikon Allah sai ka ga an sami mafitar matsalar ko kuma matsalolin.

Ya batun daura guru ko laya ko kambu a lokacin da ka ke bayar da magani ?
Lallai ban san ranar da na daura daya daga cikin abubuwan da na bayyana ba, tsabar baiwar ce na ke amfani da ita wajen ba al’umma magani, sauran bayani kuma sai in ce ma ka sirri ne tsakani na da wanda ya ba ni baiwar, shi ya sa ake kira na Malam Ibrahim Baiwa daga Allah.
Kuma ko da wani waje ne da ake ganin a kwai jinnu an kasa shiga na kan je na shiga a cikin sauki, tare da yin amfani da baiwar da Allah ya ba ni wajen warware ko wace irin matsala da ta ke addabar al’umma.
Kuma abin da zan ce ma ka shi ne mafiya yawan baiwar da Allah ya ba ni, a cikin mafarki na ke samu, da zarar na yi amfani da abin da na gani a mafarki, sai in ga an sami waraka ga matsalolin da al’umma ke kawo wa gaba, kuma sirrin baiwar ita ce biyayya ga iyaye, malamaina da duk na gaba da ni, wannan biyayya da na yi ita ma na cikin sirrin rayuwa ta da na ke amfani da ita wajen taimaka wa al’umma.

Ya batun ba masu tabin hankali magani ?
Ai wannan magana ce mai tsawo, amma abin da zan ce maka, ina taimaka wa ma su tabin hankali da magani ne domin Allah, ba domin wani abin duniya ba, saboda mafiya yawansu ni na ke kamo su da kaina zuwa gidana da ke Sabon garin NDC Rafin Guza a garin Kaduna, amma ga wadanda ke kawo lalurarsu, na kan sa wani abin da bai taka kara ya karya ba, sai dai duk da haka da kudi nake nema da wannan sana’a ta bayar da maganin gargajiya ta baiwar da Allah ya ba ni, da na tara kudi fiye da tunanin mai tuna ni, domin a wasu lokuta mutane na zuwa waje na da matsalolinsu, da alkawarin in solar sami kudi, za su biya dan abin da aka ce su bayar, amma da zarar solar sami lafiya sai su tafi, tamkar an aiki bawa garinsu, yanzu haka bashin da na ke bin al’ummomin da na ba su magani, ya wuce miliyan goma, wasu takardar alkawurran ma na ce a yayyaga su.

Kana gani ya dace gwamnati ta fara tallafa wa ma su bayar da maganin gargaji, musamman wadanda ke tallafa wa ma su lallura kwakwalwa ?
Ya dace kwarai da gaske a rika ba mu tallafin da za mu sayi maganin da za mu ba marasa lafiyar da ba su da galihu, domin a kwai wacce bayan ta sami sauki har Abuja na je da ita domin neman ‘yan uwanta, amma ban sami ‘yan uwan na ta ba haka na dawo Kaduna da ita.
………………………….

What's On Your Mind?