Yadda na rusa kuka saboda irin abin da aka rika yi mani a Barcelona – Luis Suarez

0
41
  • Luis Suarez ya bada labarin kwanakinsa na karshe a Kungiyar Barcelona

  • Dan wasan gaban ya ce an kai an daina barinsa ya yi atisaye da ‘yan wasa

  • Suarez ya ce dole ta sa wulakancin da aka yi masa ya fusata Lionel Messi

Dan wasan kwallon kafa Luis Suarez ya fito ya bayyana cewa sai da ya yi kuka a sport da yadda Barcelona ta yi waje da shi a watan Satumban nan.

Luis Suarez wanda ya bar kungiyar Barcelona ya koma Atletico Madrid a watan jiya, ya ce an kai lokacin da aka hana shi atisaye kafin ya bar kungiyar.

‘Dan kwallon ya ke cewa bai yi mamakin ganin yadda Lionel Messi ya tashi ya tsaya masa ba, a lokacin da ya fito fili ya rika caccakar manyan kulob din.

Yadda na rusa kuka saboda irin abin da aka rika yi mani a Barcelona – Suarez

“Akwai hanyoyin da za su iya fada mani cewa su na neman abubuwa su canza zani.” Inji Suarez bayan ya zura kwallo a wasan Uruguay da Chile jiya.

‘Dan wasan ya ce: “Yadda su ka yi mani, ka na jin cewa kamar ana neman kai da kai, shi ne ya fi yi mani ciwo sosai. Wadannan kwanaki ba su yi mani dadi ba.”

Tauraron ya ke fadawa ‘yan jarida: “Sai da na yi kuka a kana bin da ya ke faruwa da ni.”

Tsohon kwallon na Liverpool ya ce yadda aka kora shi daga kulob din ya masa ciwo, amma ya ce ya zama dole mutum ya fahimci cewa Duniya juyi-juyi ce.

Kalli Sabon Zazzafan Video Aisha Tsamiya Na Barka Da Safiya Zuwa Ga Masoyanta

‘Dan kwallon ya ce abin da aka yi masa, ya yi wa Messi ciwo, kuma har mai dakinsa ta lura da yadda ya zama, dole da Atletico su ka zo, ya yi maza ya tafi.

“Akwai abin da mutane ba su sani ba, amma ka je wasa a Barcelona, sai a kora ka, ka yi atisaye kai kadai, domin ba za ayi kwallo da kai ba.” Ya ce ba dadi.

Kun ji cewa duk da Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye 198 – ya zama ‘dan wasa na uku a jerin wadanda su ka fi kowa kwallaye a tarihi, an yi waje da shi.

Sabon Kocin da aka dauko, Ronald Koeman ya shaidawa ‘Dan wasan tashi ta kare a Barcelona.

What's On Your Mind?