Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin

0
33

Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya mai barin gado, Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya), ya ce hukumar Sojoji ta kwato dukkan kananan hukumomin da yan ta’addan Boko Haram suka mamaye a baya.

Ya kara da cewa hedkwatar tsaro ya samu nasarori da dama wajen inganta lamarin tsaro, kayan aikin Soji, da kuma jin dadin sojojin da ake aiki a hedkwatar.

Yayin magana lokacin da yake mika ragamar mulki hannun magajinsa, Manjo Janar Fortunate Irabor, a Abuja ranar Juma’a, Olonisakin ya zayyana irin sauyin da ya kawo hukumar.

“Za ku tuna cewa lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tya hau mulki, yan ta’addan Boko Haram suna cin karensu ba babbaka a sassan Arewa maso yammacin Najeriya, inda suka mamaye kananan hukumomi 20 cikin 26 dake jihar Borno,” Janar Olonisakin yace.

Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin

Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

“Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin da muka shiga ofis shine fitittikan yan Boko Haram tare da kwace kananan hukumomin daga hannun yan ta’addan.”

“Tare da taimakon gwamnati da mutanen Najeriya, Sojojin Najeriya karkashin jagorancina solar kwace dukkan wuraren nan dake karkashin Boko Haram.”

Janar Olonisakin ya ce duk da cewa akwai sauran matsalar tsaro a Najeriya, solar yi iyakan kokarinsu wajen aiki da gwamnati don dakile matsalar tsaron.

A bangare guda, daya daga cikin dalibai matan sakandaren Chibok, Hauwa Halim Maiyanga, ta samu yanci bayan shekaru biyar da yan ta’addan Boko Haram suka kwasheta da kawayenta.

Hauwa na cikin matan makarantan sakandaren gwamnatin mata dake Chibok, jihar Borno, ranar 14 ga Afrilu, 2014.

A cewar TheCable, wata majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa inda aka ceto daruruwan mutanen da yan Boko Haram suka sace.

What's On Your Mind?