…Yadda Muka Fatattake Su A Sabon Farmakin Rann –Rundunar Soji 

0
117

…Yadda Muka Fatattake Su A Sabon Farmakin Rann –Rundunar Soji 

Daga Muhammad Maitela,

Sojojin Nijeriya a karkashin sabuwar Rundunar “Operation Hadin Kai” ta bayyana yadda ta samu nasarar dakile yunkurin kungiyar Boko Haram a yunkurin kai sabon farmakin ta’addanci a Rann, shalkwatar karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata.

Rundunar sojojin ta bayyana haka a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaranta, Brig. Janar Mohammed Yerima, wanda ya kada baki ya ce, “Ayarin yan ta’addan solar yi yunkuri shiga garin domin su tayar da hankali ta hanyar amfani da wata kafar kan iyaka, wanda suka gamu da fushin zaratan sojojinmu a yankin tare da karon battar karfen da ya dauke su kimanin awa guda ana fafata wa.”

“Al’amarin da ya tilasta yan ta’addan ala-dole suka ranta cikin na kare da raunuka da barin makamai daban-daban masu yawa hadi da albarusai, wadanda suka kunshi bindiga mai harbo jirgin sama, bindigogi kirar AK 47, da makamantan su.”

Bugu da kari, Yerima ya kara da cewa, ”A hannu guda kuma, a ranar 2 ga watan Mayun 2021, wani gungun yan ta’addan Boko Haram solar kitsa mummunan nufin kai farmaki a kauyen Ajiri na karamar hukumar Konduga a jihar Borno.”

“Wanda ya jawo maharan solar kai ga shiga a wani bangaren garin, tare da kona gidajen jama’a guda 9 kurmus da kashe wasu mazauna garin kafin zuwan sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin.”

“Bugu da kari, a wannan dauki da sojojin mu suka kai a garin ya tilasta Boko Haram guduwa daga garin tare da mabambantan raunuka; a zazzafan martanin da suka gamu dashi.”

“Sai dai a cikin rashin sa’a, a wannan bata-kashin, sojoji biyu ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon dauki ba salon.”

“Wanda bisa ga wannan ne Hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya jinjina wa sojojin da suka nuna bajinta a kokarin hana yan ta’adda rawar gaban hantsi a yankin da suke aikin samar da tsaro.”

“Haka zalika kuma ya bukaci dakarun sojojin su ci gaba bisa karsashin da suke dashi wajen gudanar da aikin kare diyaucin kasa da al’ummar su a fagen fama.” In ji shi.

What's On Your Mind?