Yadda Mawaki Aminu Ala Ya Samu Digirin Girmamawa A Fagen Waka

0
122

Jami’ar HEGT UNIVERSITY da ke Jamhuriyyar Benin ta karrama fitaccen Mawaki Aminu Ladan Abubakar Ala da digirin girmamawa na Dakta, wanda kuma ya na daya daga cikin mashahuran mutane da jami’ar ta bai wa wannan digirin girmamawa a taron da ta shirya ranar Asabar 26 ga Satumba, 2020, a dakin taro na otel din Tahir da ke unguwar Nassarawa GRA a cikin birnin Kano.

Hukumar gudanarwar jami’ar dai, kamar yadda wakilinta ya bayyana a wajen taron, ya ce, ta bayar da lambar digirin ne ga Aminu Ladan Abubakar Ala, domin kasancewarsa mawaki da ya yi amfani da fasaharsa wajen yada adabi da kuma harshen Hausa a duk fadin duniya.

Yadda Mawaki Aminu Ala Ya Samu Digirin Girmamawa A Fagen Waka

Domin haka ne Jami’ar ta HEGT ta ga dacewar ba shi wannan lambar ta dakta, domin ba shi kwarin gwiwa a kan abin da ya sa gaba na yada adabi da kuma harshen Hausa a ko’ina cikin fadin duniya.

A lokacin da wakilin mu ya ji ta bakin Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala bayan samun wannan Digirin girmamawar, Aminu Ala ya ce “Gaskiya zan iya cewa, wannan rana abin alfahari ce a gare ni da ma duk wanda ya ke da kishin adabi da kuma yaren Hausa, domin an karrama mu ne gabakidaya.”

Ya ci gaba da cewar “Wannan karramawar zan iya cewa ta zo mini a ba zata, domin in ka kula a baya manyan mawakan da suka samu irin wannan karramawar irin su Dakta Mamman Shata da kuma Dakta Dan Maraya Jos da suka yi zaman su a baya har suka yi shaharar da aka ba su Digirin girmamawa. To kuma Alhamdulillah a wannan lokacin sai na ya zama na samu kaina a sahun mawakan Hausa da aka ba su, kuma ina ganin ni ne na farko a cikin mawakan zamani da ya samu lambar Digirin girmamawa daga dai wata Jami’a, don haka abin alfahari ne a gare ni. Kuma ina godiya ga dukkan jama’ar da suka ba ni gudummawa tun daga tasowa ta har zuwa wannan lokacin da za samu kaina a matsayin Daktan waka. ”

Ko babu komai dai idan muka duba fadi tashin mawaki Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala, za mu ga cewar ya bayar da gudummawa sosai wajen samar da wasu abubuwa da za a iya kallon su a matsayin Juyin juya hali a cikin harkar wakoki na zamani.

Domin kuwa shi ne mawakin zamani na farko da ya fara shiga fadar Sarkin Kano ya yi kida da kayan zamani, a lokacin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya cika shekaru 45 a kan Sarautar Kano. Wanda kuma daga wannan lokacin ne Sarakunan Arewa suka karbi mawakan zamani a matsayin mawakan su har suka fara gayyatar su wajen taron bukukuwan su.

Baya ga wannan shi ne mawakin zamani na farko da ‘yan siyasa suka fara yin amfani da wakar su ta hanyar tafiya da shi wajen yakin neman zabe, wanda hakan ya fara ne a lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, aka yi amfani da wakokin Aminu Ladan Abubakar Ala, wajen tallata manufofin shirin A daidaita Sahu da kuma yakin neman zaben 2007.

Ta Fannin kasuwancin wakoki ma Aminu Ladan Abubakar Ala ya kawo sauyi inda ya kasance mawaki na farko da ya sauya fasalin kasuwancin wakokin Hausa na zamani ta hanyar tallata su a kan Mota ana a cikin gari da wajen tarukan jama’a, sannan ya samar da tsarin Jaket na zamani da a ke amfani da shi.

Baya ga haka shi ne mawakin zamani na farko da aka nadawa rawani a Fadar Sarkin Kano. Wanda kuma bayan wannan ya samu sarautar Dan Amanar Bichi Dijimin Masarautar Karaye, Sarkin wakar Masarautar Dutse. Yanzu kuma ga shi a matsayin (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala.

What's On Your Mind?