Yadda matasa suka kona ofishin yan sanda a jihar Sokoto

0
133

Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da konewar wani ofishin yan sanda da wasu motoci biyu a karamar hukumar Kware.

BBCHAUSA ta ruwaito,Mai magana da yawun rundunar yan sandan ASP Abubakar Sani cikin wata sanarwa ya ce lamarin ya faru ne bayan da wasu gungun mutane suka je chaji ofis din inda suka nemi a saki wasu mutum biyu da ake zargi masu garkuwa ne.

Sanusi ya ce tun farko an kama wadanda ake zargin inda ake gudanar da bincike a kansu saboda samunsu da hannu a garkuwa da mutane a yankin.

Ya bayyana cewa gungun akasarinsu matasa solar je ofishin yan sandan inda suka rika ihu tare da neman a saki mutanen biyu da ke tsare.

Kakakin rundunar ya kara da cewa mataan solar ci karfin jami’an tsaron da ke kula da ofishin inda suka cinna masa wuta har da motar DPO da wasu motocin yan sanda biyu.

A cewarsa, matasan solar halaka daya daga cikin mutanen da ake zargi masu garkuwa ne tare da raunata dayan.

Kawo yanzu, ba a kama ko mutum daya ba amma ana ci gaba da gudanar da bincike.

What's On Your Mind?