Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Shimfida Tsarin Gina Kasa A Madina Bayan Hijira

0
118

Masu karatu Assalamu warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. A makon da ya gabata, mun ji irin alherai da ke cikin Hijira na daga ‘yanci da kafa kasa da gina kasa duk da sunan ‘yan kasa, da sunan Musulunci yadda Manzon Allah (SAW) da Sahabbai suka samun ‘yancinsu suka kafa kasa, suka kafa bukukuwansu irin su sallolin idi da sauransu.

A farkon dawowa Madina, akwai ‘yan kasa da aka samu wadanda ba musulmi ba, wasu Yahudawa ne, wasu Nasara, wasu Maguzawa, amma sai Annabi (SAW) ya yi tsarin zama na kasa da bai wa kowa ‘yanci don a zauna lafiya. Daga baya, daga Allah, Yahudawan suka warware alkawari, aka kori Banud Nadir da kainuka’a, aka kashe kuraizata saboda photo voltaic yi ha’inci, photo voltaic ha’inci kasa a lokacin yaki. Duk wanda ya yi wannan kuma, ya ha’inci Allah, ya ha’inci Manzon Allah (SAW).

kasar da wasu ke ganin ba komai ba ce, Manzon Allah ya ce duk wanda ya ci kasar makocinsa kamu daya, ya ci har kasan bakwai, kuma za a yi wa mutum rawani da ita a jefa shi a wuta ranar tashin kiyama. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda aka kasheshi a fagen yakin kare kasarsa Shahidi ne, ba za a ce mutum ya mutu a banza ba saboda ya mutu a kan kare kasa.

Haka nan duk wanda ya ha’inci Musulunci a matakin Islam, ko darika a matakin Iman da Faila a matakin Ihsan, ya ba da kofa aka yi sharri, maimakon ya kare sai ma ya rika ruruta abin, to ya ha’inci Allah da Manzon Allah (SAW).

Manzon Allah ya koyar da mutane yin ado da kwalliya, akalla a yi wanka sau daya a sati kamar yadda ya nunar a ranar Juma’a. Hatta kasuwanni sai da Manzon Allah ya kakkafa cikin tsari. Wannan duk yana daga cikin albarkar Hijira saboda ‘yancin da aka samu. Sannan da rarraba aiki, masu hali su taimaki marasa shi, su kuma marasa hali kar su yi girman kai su girmama masu hali su taimake su cikin aikinsu.

Manzon Allah ya zo ya tarar da ‘Yan Madina a kasarsu, da gonakinsu, sannan ga wadanda suka zo daga Makka su kuma, wadansu photo voltaic zo da wani abu (na dukiya) wasu kuma ba su zo da shi ba, sannan ga wasu ‘Yan Madina an samu sashinsu yana gaba da wani sashi.

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Shimfida Tsarin Gina Kasa A Madina Bayan Hijira

Manzon Allah sai ya cire sunan gaba a tsakanin mutanen da ke gaba da juna na Madina (Ausi, Khazraju da sauransu) bakidaya, ya sa musu sunan ‘Ansaru’ (Mataimaka), ya cire sunan ‘Yasriba’ ga kasar ya sa mata ‘Madina’. Kuma duk abin da yake jawo gaba Manzon Allah ya cire.

Haka nan ya koyar da yadda za a zauna lafiya tare da wadanda ba musulmi ba a kasar. Shi ya sa duk in ka ga musulmi ya shiga wani rikici ya kauce wa karantarwar Manzon Allah (SAW), to wannan kuma sai a ce ‘La haula wa la kuwwata illa billah…’

Hadarin da ake ciki yanzu shi ne akwai wadanda suke koya wa yara sabanin abin da Manzon Allah ya koyar na zamantakewa, suna ganin koyarwar tasa (SAW) kamar sakaci ne, sai su ne za su koyar da kishin islama da fushi da zage-zage, wato a ganinsu wancan na Annabi ba kishi ba ne. Ga shi har an kai abin da aka kai yau, Allah ya gyara mana.

Mutanen Madina suka ce za su raba dukiyoyinsu biyu su ba Muhajirai, su kuma suka ce a’a, ku rike dukiyoyinku, suka zabi su yi aiki tare da su a cikin dukiyoyin suna raba ribar abin da aka samu a tsakaninsu, da haka suka iya kasuwanci kuma dama wasunsu photo voltaic iya kasuwancin tun a Makka. Sayyidina Abdurrahman bin Auf an hada shi da wani mai kudin Madina, ya ce masa zai raba dukiyarsa biyu ya ba shi rabi, ya shiga ya duba a cikin matansa ya zabi wacce ta yi masa zai saketa shi ya aureta (irin wannan sai a wurin Almajiran Manzon Allah ake gani ko Kalifansa Sahibul Faidhati).

Nigeria 0-1 Algeria (Wasan kwallon sada zumunta)

Abdurrahman ya ce masa Allah ya yi wa dukiyarka albarka, Allah ya yi wa matanka albarka (ka rike) ni dai nuna mun kasuwa kawai. Shikenan ba a dade ba bayan ya fara kasuwanci sai ga shi ya zo gaban Manzon Allah da kunshi a hannu, har ya yi kudi ya yi sabon aure.

Lallai talaka ya girmama mai shi, domin Manzon Allah ya ce talaka mai girman kai ba zai shiga Aljanna ba (ana jin kamshin Aljanna kimanin tafiyar shekara 500, amma shi ba zai ji ba, ga talauci ga girman kai ai kuma duk bala’i ya faru).
To haka ya kasance, su masu kudin ba su da rowa, su kuma talakawan ba su da girman kai da nuna butulci. Yana daga abin da Manzon Allah ya yaka; rowa, bare kuma zalunci da ba da bashi da ruwa da danniya ga talakawan kasa kullum a take su a kasa, duk Manzon Allah ya yaki wannan.

Ya ci girman Almajiran Manzon Allah (SAW) wannan Haidisin da muke ta karantawa, mu gaya wa Turawa da duk wani ma da yake alfahari da kansa. Hadisin nan da Talakawa suka zo wurin Manzon Allah (SAW) suka ce Ya Rasulallahi, masu kudi photo voltaic tafi da lada, suna sallah kamar yadda muke yi, kuma mafificin kudin nasu shi suke ba mu (sadaka).

Ma’ana talakawan photo voltaic kawo kara kan cewa masu kudin suna da wani abu da suka fi su da shi a wurin Allah. Suna ibada iri daya yadda suke yi, sannan photo voltaic dara musu da sadaka. Manzon Allah sai ya ce wa talakwan ku je ku yi ta Zikiri da yawa shi ma sadaka ne, Manzon Allah ya lakana musu ‘Subhanallah…’, ai da masu kudin suka ji su ma sai suka kama yi, talakawan suka kara komawa wurin Manzon Allah suka ce abin da ka ba mu su ma masu kudin photo voltaic kama suna yi.

Sai Manzon Allah ya ce “wannan falala ce da Allah yake ba wanda ya so”.
Alhamdu lillah, irin haka ‘Yan Faila Almajiran Shehu Ibrahim na gaskiya suke. Duk ibadu na Allah da talakawan ke yi su ma masu kudin suna yi. Kuma sai dai talakawan cikinsu su yi kishin darajarsu a wurin Allah (ba hassada ba). Duba dai irinsu Alhaji Maigemu Gusau, Alhaji Uba Ringim da Khalifanmu Shehu Isyaka Rabi’u, tun daga cikin kasar nan har zuwa waje za ka ji ana labarin irin alkharain da ‘Yan Failan suka yi. Dubi irin su Shehu Salisu Mu’azu da Shehu Lawal Bara’u, ga Shehu Audu Kwangila a Kaduna. Allah ya dawo da masu kudin nan a cikinmu Albarkar Annabi (SAW).

Wannan duk tunatarwa ce, saboda kowa yana jin tarihin alkhairan da magatansa suka yi zai ji dadi.
Manzon Allah (SAW) ya yi hijira ba tare da ko kobo ba, haka kuma ya shiga gaba wurin aiwatar da duk tsare-tsaren gina kasa da yake shimfidawa, Daula ta ginu, Duniya ta canju. A cikin tsarin ne Manzon Allah ya gina Masallacinsa, kuma dama duk inda Musulmi yake Masallaci ne kan gaba a wurinsa. Masallacin Manzon Allah ya kasance nan ne wajen aike (na manzanci), nan ne wajen shawara, nan ne wajen haduwa da baki da sauran harkoki.

Daga nan sai kuma Manzon Allah ya gina ‘yan’uwantaka wanda shi ne babban ginshikin bayan hijirar, da Muhajirai da Ansaru suka zama ‘yan’uwan juna, kuma tun daga nan abin ya sport, Musulmi ya zama dan’uwan Musulmi har tashin duniya. Manzon Allah ya yi wannan domin ya tafiyar da jahiliyya da kabilanci da bambancin launin fata, ya zama babu wani abu da zai daukaka mutum ko ya kaskanta shi sai tsoron Allah. Rashin tsoron Allah shi zai kaskantar da mutum ya sa ya yi baya.

Sannan Manzon Allah ya kafa dokokin da suka kiyaye barna, suka kiyaye jinin al’umma. Haka Manzon Allah ya tafiyar da al’umma cikin tsari tare da karantar da su da Alkur’ani da Zikirai da sauran abubuwa na shiriya har Allah ya kawo zamanin Faila aka ga Zamanin Manzon Allah (SAW) a sarari. Mutanen kudancin duniya, da arewaci, da yammaci da gabashi suka narke cikin ‘yan’uwantaka na Allah. Idan mutum yana neman gaskiyar wannan ya dau Goran Faila ya karanta (idan ba ya jin Larabci sai Hausa), idan kuma yana jin Larabci ya dau Mir’wakul Ishak wanda Bayin Allah da suka riski zamanin suka rubuta. Ba su ne kadai ba akwai su da dama, amma dai wadannan su ne jagorori. Ka tsaya ka karance su da kyau zuciyarka a bude komai zai fito maka a sarari in dai ba hayaniya kake so ba. Alhamdu lillah, komai a sarari yake.

Haka nan Shehu Ibrahim littafan da ya rubuta irinsu Kashiful Ilbas da sauran hudubobinsa duk saboda tausayinsa ya saukaka bayanai ta yadda manya da kanana kowa zai gane. Ga kuma yanzu Khalifa Shehu Tijjani Inyass ya nemi Larabawa su fito da abubuwa na Shehu da ke wurinsu saboda masu tasowa da muradinsu shi ne Allah. Kuma Alhamdu lillah, ga Muhammadu Abdullahi dan Shehu Jejiba nan ya dukufa, ko zuwa yanzu ya fitar da littafan kayan Shehu photo voltaic fi 20.

What's On Your Mind?