Yadda Kungiyar Jama’atud Da’awa Ta Gabatar Da Taron Lacca Da Shan Ruwa A Abuja

0
86

Yadda Kungiyar Jama’atud Da’awa Ta Gabatar Da Taron Lacca Da Shan Ruwa A Abuja

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Duk burin Iyaye shi ne suka cewar ‘ya’yansu solar tashi cikin tarbiyya wadda ko bayan babu ransu ba za a rika fadar maganganun da basu dace ba, kan  hanyar da suka sa ‘ya’yansu  manufar tarbiyyar ko wacce  irin nau’i ce suka basu. Bama kamar wannan zamani ko lokacin da ake ciki  na yadda wasu ‘ya’yan ko, an koya masu tarbiyar ba amfani suke da ita ba, sai dai a rika bin su da addu’a bayan an sa su a hanya madaidaiciyar, wadda ita ce bin tafarki na addinin musulunci ne duk kokarin da ake. Halin da ake ciki yanzu sai dai iyaye su yi iyakar kokarinsu, sauran kuma su bi ‘ya’yansu da addu’a da kuma bar ma Allah madaukakin Sarki ya yi na shi ikon.

 

Da take zantawa da manema labari ciki har da Jaridar MOBILIZED9JA AYAU Mrs Rakiya S. Bamalli ta bayyana cewar ita manufar shirya laccar ta shan ruwa a wata mai tsarki na Ramadan ita ce, an fara gabatar da ita laccar shekaru bakwai da suka gabata. Ga kuma bukatar su samu hadin kan junansu, bugu da kari kuma su yi koyi da wadansu abubuwan da Shugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihis Wasallam, ya hore mu da cewar mu yi.

 

Da aka tambaye ta an lura da cewa su wadanda suka gabatar da laccar duk matasa ne, sai ta bada amsar cewar su a matsayin su na Iyayen sune suka fara yin wannan al’adar shekaru bakwai da suka gabata. Ta kara bayanin cewar da hakan ne za su rika jawo hankalinsu ‘ya’yan nasu da lurar da su kan abubuwan da suka dace na rayuwa ta hanyar addinin musulunci.

 

Ita kungiyar Da’awa tana karskashin makarantar Fu’advert Lubabidin shekaru ashirin da daya ke nan da kafa makarantar Islamiyyar ta mata, an kafa ta ne saboda hadin kai na musulmi dama wadanda ba musulmi ba, kamar yadda ta riga ta yi bayani,mazauna Abuja dama wadanda ba mazauna  birnin na Abujar ba.

 

Ta kara jaddada cewar suna zuwa kauyuka suna jan hankalin mutane wadanda ba muslmi ba, suna koyar da su addinin musulunci, su taimaka masu har ma da wadanda ba musulmi ba.

Da aka yi mata tambayar ganin yadda ake da kungiyoyin musulunci daban- daban na musulunci ya maganar zama dan kungiyar tasu ta Da’awa yake, sai ta ce idan dai mutum musulmi ne, to yana cikin wannan kungiyar.

 

Har ila yau dangane da su dai matasan ta ce al’amuran nasu suna karkashin kulawar kungiyar Da’awar ta mata, ta ce solar yi hakan ne domin sannu a hankali suna jawo hankalinsu, wajen koya masu abubuwan da suka dace su rika yi na addinin musulunci, bayan kuma solar riga solar basu ilimi, kuma kamar yadda watarana su matasan, sune za su ci gaba da inda suka tsaya, saboda halin rayuwa, sai su matasan su ci gaba daga inda suka tsaya. Abin kuma yana da bada kwarin gwiwa ganin yadda su matasan suka tafiyar da harkokin aiwatar da ita laccar ta shan ruwa, suna sa su a gaba ne, da kuma basu duk gudunmawar da suke bukata.

 

Ga sauran kungiyoyin addinin musulunci kuma ta basu shawarar cewar su yi kokari su hada kai domin kira zuwa ga al’amuran addinin muslunci.

 

Malamai biyu sune suka gabatar da lacca kafin a kai ga shan ruwa akan me ake nufi da nasara a addinin musulunci , da kuma abubuwan da suka kamata mutum ya rika aikatawa, cikin saura kwanaki goman da suka rage na watan Ramadan saboda, bukatar da kowa yake da ita, ta ya sadu da shi darennan mai albarka na Lailatul kadar. Malaman sune Muhammad Abdalla da kuma Muhammad Zahruddeen Usman.

 

 

What's On Your Mind?