Yadda Karamar Sallar Bana Ta Zo Wa ‘Yan Nijeriya Cikin Tsoro Da Tsada

- Advertisement -

Yadda Karamar Sallar Bana Ta Zo Wa ‘Yan Nijeriya Cikin Tsoro Da Tsada

Ga dukkan alamu karamar sallar bana ta zo wa ‘Yan Nijeriya a wani irin yanayi na gaba-kura-baya-siyaki saboda tsadar rayuwar da ake fuskanta da kuma matsaloli na tsaro. Wakilanmu da ke sassan arewa solar yi mana rahoto na musamman a bisa yanayin da sallar ta zo wa ‘yan kasa kamar haka:

 

…Tsadar Kayan Masarufi Da Tufafi Ta Sa Wasu Za Su Yi Sallah Lami A Kano

 

Rashin Karbar dinkunan Sallah Ya Bar Telolin Da Tagumi

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

 

Kasancewar yau take Sallah karama wadda hakan ke nuni da kawo karshen azumin watan Ramadan na wannan shekarar, abubuwan da a halin yanzu ke gaban magidanta bai wuce batun kayan sallar yara da kuma abincin da aka saba dafawa a irin wannan rana ba. Amma sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi ba Kano kadai ba har ma da kasa baki daya, ya sa zuwa yanzu da yawa wasu iyalan ba su san makomar kayan sallar yaransu da iyalai ba, musamman yadda kudin dinkin ya yi wuya kwarai, sakamakon abinda tilolin ke cewa kayan dinkin duk solar yi tashin gwauron zabbi a kasuwa.

 

Wani Tela da ya bukaci na sakaya sunansa dake sansanin teloli a unguwar Fagge cewa ya yi, yanzu shi har tsoron shiga gidansa yake, domin yaransa wadanda ke iya zuwa shagonsa suna ganin yadda shagon ke cike da dinkuna, amma kuma ba su san cewar dinki ba kudi ajiye ce kawai ba, sannan kuma idan solar koma gida suna fada wa iyayensu mata cewar shagon baba cike yake da dinkuna, don haka kenan aljihuna nima a cike yake da kudi, kuma duk bayanin da zan yi ba dole su fahimce ni ba.

 

Haka lamarin yake a bagaren kayan abinci musamman shimkafa da kayan gwari, da farkon azumi kamar a wannan karon ba za’a gamu da karancin kayan gwari ba, amma yanzu solar zama gwal, sai mai hannu da shuni ne kadai ke iya sayen danyan tattasai, Tomatiri, attarugu da albasa, amma ‘yan rabbana ka wadata mu dama dai kwanakin karshen azumi da fara da mai aka lallaba aka karasa. Saboda haka kila wasu su fara Sitta Shawwal ba tare da bata lokaci ba, kasancewar babu alamun samun wani muwalati a wannan karon.

 

A bangaren ma’aikata kuwa al’amarin sai dai ayi addu’a a tashi domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto wasu ma’aikatan ba suyi hafzi da albashin watan da ya gabata ba, sannan kuma daman akwai mummunan ciwon zaftare albashin ma’aikatan da aka fuskanta a watannin baya, harma anji Gwamnati na neman sa zare da kungiyar kwadago kan yunkurin Gwamnatin Jihar Kano na komawa tsohon matakin albashi na Naira dubu goma sha takwas (18,000.00). Saboda haka daman ma’aikata na cikin tsaka mai wuya, da farko dai solar gamu da yanke yanken albashi, sannan kuma dan karin da akayi na mafi karancin albashi a Jihar Kano na Naira dubu 30,600,00 ya gagari Gwamnatin ci gaba da biya, sakamakon abinda suka bayyana da cewa an samu raguwar kason da ake samu daga Gwamnatin tarayya.

 

Saboda haka yanzu wasu ma’aikatan ba tama karamar sallar suke ba, a’a abinda da za’a sa abakin salati shi ne babbar bukatar su. Amma dai har yanzu ma’aikatan basu yanke tsammanin samun albashin ba, musamman ganin JIhar Kano ba’a taba batan watan biyan albashi ba tun zuwan Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

 

A bangaren shagulgulan sallah kuwa, a wannan shekarar ba kamar shekarar information gabata ba, anji masarautar Kano na shelanta cewa za’a gudanar da hawan sallah kamar yadda aka saba, wanda a shekarar information gabata annobar Korona bata bari komai ya gudana ba. Sai dai ko yanzu ma anji sanarwa na nuni da cewa an rufe gidajen wasanni da sauransu, musamman jin alamu sake wannan mummunar annoba.

…………………..

Bikin karamar Sallah A Kaduna: Yadda Rashin Kudi Zai Hana Sallar Armashi

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

 

Kasancewar akwai rashin wadatar kudade a hannun al’umma ciki har da ma’aikatan Jihar Kaduna, hakan ya janyo koma-baya ga armashin bikin karamar Sallah ta bana.

 

Idan muka waiwayi Ma’aikatan Gwamnati musamman wadanda a halin yanzu suke cikin tsaka mai wuya, kasancewar yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallame su daga aiki, da kuma wadanda suka kwashe tsawon watanni ba tare da an biyasu albashin da hakkokinsu ba, da kuma tsofaffin ma’aikata ‘yan fansho wanda su tuni solar fara sallama ko bar ma Allah hakkokinsu dake hannu Gwamnatin Jihar Kaduna, kasancewar irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanyasu a gaba wajen bin diddigin tantance hakkokin su babu dare ba rana, amma har yanzu shiru kakeji, wai malam ya ci shirwa.

 

Su kansu ‘yan kasuwar Jihar Kaduna musamman wadanda Gwamnatin ta tashe su, ko ta rushe masu wajajen sana’arsu, da kuma saura daidaikun ‘yan kasuwar, dukkaninsu solar ko ka dangane da mawuyancin halin rashin kudin da suka tsinci kansu na rashin samun mutanen da ke zuwa yin sayayyar sallah.

 

Wani Ma’aikacin Jihar Kaduna mai suna Malam Adamu Aliyu Ahmad da ke aiki da hukumar Ilimi ta jihar, ya bayyana wa MOBILIZED9JA AYau cewa, “kasancewar har yanzu ana ci gaba da aikin tantance ma’aikata a fadin wannan jiha, hakan ya jefa ma’aikata cikin halin kuncin da rashin tabbas, saboda a maganar da nakeyi da kai a yanzu, ina tunanin ba’a tantance sama da kashi 40 cikin 100 na ma’aikatan wannan jiha ba, kuma yadda dokar take shi ne, har sai an tantanceka kafin a ba ka cekin kudin albashinka na wata daya a hannunka.”

 

Malam Aliyu ya kara da cewa, “ka ga kenan wasu ma’aikatan babu yadda za a yi a ce solar sami albashinsu a hannu kamin sallah, dole ne ta sanya sallar bana rashin yin armashi, mussamman yadda al’umma ke kukan rashin kudade a hannunsu. Saboda haka ina kira da kakkausar murya ga mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad el-Rufai, da ya dubi Girman Allah, da girman wannan wata mai tsarki, ya daga wannan dokar ta tantancewar har sai idan Allah ya kaimu bayan sallah, saboda hakan zai iya baiwa ma’aikata damar samun albashinsu cikin sauki, domin gudanar da bukukuwan sallah cikin jin dadi da kwanciyar hankali.” In ji shi.

 

Amma duk da rashin yawaitar kudade a hannun al’umma, amma hakan bai hana wasu al’umma jajircewa wajen ganin solar wadata iyalansu da sababbin dinkunan sallah ba, mussamman kasancewar al’adar sallah karama shi ne yin sababbin dinkuna ga wanda Allah ya ba su hali.

 

Wani tela mai suna Yusuf Haruna, ya bayyan awa MOBILIZED9JA AYau cewa, “gaskiya akwai matsalar rashin kudi sosai da ya addabi Al’umma mussaman kasancewar yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallami duban ma’aikatan jihar, wanda kusan kashi 65 na mazauna Jihar Kaduna, ma’aikatan Gwamnati ne, a dalilin Jihar Kaduna na zama cibiyar Arewacin kasar nan.”

 

Yusuf ya kara da bayyana cewa” Amma abin mamaki shi ne, duk da matsalar rashin kudi a hannun jama’a, amma hakan bai hana wasu iyaye jajircewa wajen ganin su share ma Iyalansu hawaye wajen ganin solar wadata iyalan nasu da sababbin tinkuna sallah, saboda yin hakan ya zama wani babbar al’ada.”

 

Ya kara da cewa, “ina mai tabbatar maka da cewa, tun ana Sallah saura wata daya na rufe amsar dinki daga hannun mutane, kasancewar mun tara dinkunan har solar yi yawa. Sannan a bangare daya kuma, gaskiya mu na fuskantar babban kalubale wajen biyanmu hakkokinmu, kasancewar babu kudi a hannun al’umma, duk yawancin wadannan dinkunnan da kake gani, idan mun yi, duk kusan a bashi suke tafiya, saboda rashin wadatattun kudi a hannun jama’a.” A cewar Yusuf Haruna.

…………………

…Yanayin Yadda Za A Yi Sallah karama A Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Masarautar Daura ta fara bada sanarwa ta dakatar da duk wasu bukukuwan Sallah a wannan karamar Sallah saboda abinda ta kira rashin tsaron da ake fama da shi a jihar Katsina da kuma wasu jihohin arewacin Najeriya.

Bisa ga wannan dalili da masarautar ta bada, sai hankali ya koma akan masarautar Katsina domin ita ba ta ba da sanarwa ba, haka ya sa ake tunanin za a gudanar da shagulgulan bikin Sallah karama a wannan a masarautar Katsina

Sakamakon yadda matsin lambar tattalin arziki ke kara shafar duk wasu al’amura da suka shafi al’umma, hakan tasa dole komi yanzu sai an duba sannan a ga me yakamata ayi me ya kamata a bari, saboda yanayin yadda aka tsinci kai a wannan lokaci.

Alal hakika tsadar rayuwa da kuma halin kunci da mafiyawan jama’a suka shiga ya sauya fasalin yadda suke gudanar da bukukuwan Sallah a jihar Katsina musammnan karamar Sallah wanda ita ce ake yi wa tanadi fiye da babba.

To sai dai kamar yadda na ambata a sama cewa kullum abubuwa suna kara canzawa saboda hatta ita kanta Sallah tana zuwa ne da wani sabon salo, wani lokacin ta zo wa jama’a aljihunsu shar wani lokacin kuma sai a hankali.

Jihar Katsina ta shiga wani yanayin na rashin yin bukukuwan Sallah kusan shekaru biyu ke nan sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa jama’a ba dare ba rana, wannan yasa abubuwa duk solar sauya matuka musamman a irin wannan lokacin na Sallah.

Kamar yadda aka sani kuma tarihi ya nuna garin Katsina na daga cikin sahun farko na manyan garuruwan kasar hausa da ke gudunar da shagulgulan Sallah sai dai kash shekara kusan biyu kenan wannan gari na Katsina yana cin karon da matsala.

Sace mutane 40 da ‘yan bindiga suka a loakcin Sallah Tuhaju a garin jibia da ke jihar Katsina na daya daga ckin dalilna da yasa masarautar ta Katsina ta yi dogon tunani tare da tuntubar masu ruwa da tsaki domin dakatar da wannan hawan Sallah

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata sakamon bullar cutar mashako da tsarke nunmfashi da kuma hare-haran ‘yan bindiga tasa dole aka dakatar da wannan gagarumin bikin hawan Sallah da aka saba gudanarwa a garin Katsina

A kusan karo na biyu hakan tana faruwa domin kuwa a ranar litinin masarutar Katsina ta ba da sanarwar dagakatar da duk wasu shagulgulan Sallah inda ta bayyana cewa ta yi hakan ne domin duba da yanayin tsaro bayan ta yi doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan sha’anin tsaro a karshe dai an dakatar.

Wannan bakin labari ya sauya al’amura da dama a garin Katsina musamman jama’ar da suka shirya tsaf domin huce haushin hawan Sallah da ba su yi ba a baya, sakamakon abubuwan da na ambata sama.

Lallai a wannan karon dai kam abun babu dadin bayyanawa domin kuwa duk wanda yasan yana da sha’awar kallon ko shiga cikin wannan ruguntsumin Sallah to ya riga ya iso Katsina `

Duk da wannan sanarwa da masarautar Katsina ta fitar hakan bai hana mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman bayyana cewa za a yi Sallar Idi kamar yadda aka sabo, abinda kawai ba a za ayi ba shi ne hawan Sallah da hawan dawakai kamar yadda aka sabo yi duk Sallah

Wani abin ban tausayi shi ne yadda jama’ a ke fama da rashin kudi ganin cewa hatta albashi gwamnati ta yi shi ne da kyar da karfin hali a wannan wata saboda haka bikin dai zai kasance kadaran kadahan.

………………………………….

A Bauchi Ba Yabo Ba Fallasa….

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A daidai lokacin da al’umma suke shirye-shiryen bukukuwan Sallah a Nijeriya, a jihar Bauchi za a iya cewa tunin wasu rukunin jama’a suka fara domin a jiya wasu ba’adi na jama’a solar gudanar da Sallar Idinsu tare da bude baki a fadar jihar wanda hakan ke nuni da cewa tun a jiya aka fara shagula.

A bangaren yanayin gari, jama’a solar misalta yadda sallar bana ta zo musu da cewa babu yabo babu fallasa, kuma dai kawo yanzu a bangaren yanayin tsaro ana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yayin da jama’a ke cigaba da hada-hadar sayen kayayyakin abinci da na kwalliya domin faranta ran Musulmai.

A fannin walwala wasu na kan fara’a a yayin da wasu ma’aikata wadanda suka kasance ‘yan kalilan ke korafin rashin samun albashi sakamakon aikin tantance ma’aikata da ake cigaba da yi, duk kuwa da cewa gwamnatin jihar ta biya albashi wanda ke nuni da cewa akwai walwala na kudade a hannun jama’a, su kuma rukunin wadanda basu samu albashi ba na cigaba da nuna korafinsu da rashin walwala sakamakon dogara da suka yi da fannin albashi.

To sai dai a binciken wakilinmu akwai cigaba na walwalar kudade da kwanciyar hankalinka a wajen jama’an jihar fiye da na shekarar da ta gabata, sannan kuma ba a samu tashin farashin kayan masarufi fiye da kima ba, hakan ya baiwa jama’a damar samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

A fannin kasuwanni, kamar kowace shekaru masu fitowa domin cin kasuwar sallah na musamman suna cigaba da cin kasuwancinsu a bakunan hanya da wasu kebantattun wurare wanda sukan karya farashi domin jama’a su yi ribibin saye.

A fannin tsaro kuwa, Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bada tabbacin inganta tsaro da kare rayukan jama’an jihar a yayin bukukuwan sallar Idi.

A wani sanarwar da Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi Sufuritandan Ahmad Muhammad Wakil, ya bayyana cewar an tanadar da ‘yan sanda three,147 da za su yi aikin wanzar da tsaro a cikin masallatan da za a yi sallar idi a fadin jihar.

Baya ga su, ya kuma bayyana cewar akwai sauran hukumomin tsaro da zasu hada kai wajen tabbatar da an yi sallar lafiya da gudanar da shagulan bikin sallar lafiya.

A fannin hawan Daushe da na Sallah mai cike da tarihi a masarautar Bauchi kuwa, yana nan kamar yadda aka tsara kuma aka saba duk shekara.

Hawan Daushe na daga cikin muhimman abubuwan da jama’a ke yi domin samun nishadi da annashuwa a bikin sallar kowace Idi.

A bisa ingancin tsaro da ke da akwai, jama’a na cigaba da kara azama wajen ganin solar faranta ran iyalansu.

Wakilinmu ya ji ra’ayin wasu jama’an jihar kan wannan bikin sallar, “Eh gaskiya alhamdullahi na samu na yi wa ‘ya’yana dinkin Sallah kuma ‘yan gaji da shinkafar da ake dafawan nan dukka dai mun samu mun tanadar,” inji Gambo Isa, wani mazaunin Gwallaga a cikin garin na Bauchi.

“Muna fatan cewa za yi bikin a kare lafiya, kuma da fatan Allah ya amshi addu’o’i da ibadunmu. Batun walwala sai godiya domin in ka lura kasuwanni da wuraren gudanar da saye da saidawa duk solar cika a daidai lokacin da nake wannan maganar da kai, don haka sai godiya da fatan a yi komai lafiya,” Inji Sulaiman Ahmad, wani ma’aikaci a jihar.

………………………..

…Mutanen Neja Za Su Yi Sallah Cikin Fargabar ‘Yan Bindiga Da Tsadar Rayuwa

 

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

 

A daidai lokacin da watan Ramadan ya cika kwanaki talatin cif, yayin da ake bukin sallah karamar ranar alhamis din makon nan. Yanayin dai bài zo wa mafi yawan jama’a cikin dadin rai ba, musamman bayan fargabar mahara masu dauke da bindiga da suka zama barazana da kwashe dukiyoyin jama’a, ga tsadar rayuwa na kayan masarufi da jama’a ke ji a jikinsu.

Wani abinda yafi shafar rayuwar al’umma a wannan hidimar sallah musamman ga mafi yawan jama’ar jihar da suka dogara da albashi, yanayin bai canja ba, domin kamar sauran watanni baya ne da ma’aikatan ke dandana kudarsu ta hanyar zaftare albashi daga matakin kasa zuwa sama mafi yawa solar shaidi wannan zaftaren da bai kan ka’ida.

Baba Ali, wani ma’aikaci ne da ya nemi a sakaya ma’aikatarsa yace ina karban albashi kusan dubu arba’in ne amma dubu biyar da ‘yan matsabbai na gani a cikin asusun ajiya ta da sunan albashi, ni ban ci bashi ba balle a ce an cire, yanzu maganar abincin sallah ma da ya zama wajibi ban san ta inda zan fara ba, maganar gaskiya idan ba ta canja zani ba gwamnati za ta jefa mutane cikin kakanikayi akan lamarin sallar nan, gobe ne fa sallah kuma da yawan mu ba wanda yai komai a gida.

Malam Umari Sabon Titi kuwa cewa yayi maganar sallah, muna addu’ar Allah ya kai mana rai lafiya kawai, domin mu da kan hada kudi mu sai dabbar yanka bana lamarin sai addu’a.

Saniyar da muka saye dubu dari da sittin da biyar a bana, a shekarar da ta gabata ko tai tsada ba ta wuce dubu dari ko da goma, dabbobi ba su tabuwa, kaji ma ba su tabuwa abin dai sai addu’ar Allah ya kawo mana sauki.

Malam Nura Rijau, wani Tela ne mai zaman kan shi, yace bana ba yabo ba fallasa domin an samu aiki daidai wa daida, ina da tabbacin wasu shaguna ba zasu kammala dunkunan da suka amsa ba.

Maganar gaskiya mutane na kukawa sosai, domin ko irin rabon abincin nan da ake yi bana kamar an ruwa an dauke sai dai can ba a rasa ba, kuma ina ganin hakan ya samu asali ne a irin tafiyar da shugabancin jihar daga ‘yan siyasa.

Domin mafi yawan su solar gudu umura, wadanda kuma ke nan sai faman buya suke yi, na ji kuma irin yankan kaunar da aka yiwa ma’aikata ta hanyar zaftare albashin mafi yawan su, wanda su kan su ‘yan kasuwa da su ne suka dogara, to gaskiya za a yi sallah ne a cikin matsi.

Sidi Shareef Ishak Tudun Fulani, kuwa jawo hankalin shugabannin yayi muhimmancin taimakawa talakawa da masu rauni musamman kananan ma’aikata da suka dogara da albashi, yace gaskiya ya kamata shugabannin su rika jin tsoron Allah suna taimakawa talakawa, ga dukkan alamu sallar bana tazo da wani yanayi na daban, ga talauci da jama’a ke fama da shi musamman ma ‘yan gudun hijira sannan ga kudade ba sa yawutawa balle su kai hannun wadanda ba su da shi.

Muna fatar Allah ya ba mu ikon cin wannan jarabawar, dan ana cikin jarabawa gaya.

………………….

 

…Rashin Abinci Da Tsadarsa Zai Takura Shagalin Sallah A Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

 

Al’ummar Jihar Zamfara, solar dogara ne da noma da kiwo, don shi ne ginshikin tattalin arzikinsu wanda manyan manoma da matsakaita suka dogara da su,sai gashi yanzu abin har ya fara kai ga ya gagara,sakamakon yadda ‘yan bindiga su ke cin karensu babu babaka a fadin Jihar Zamfara. Wannan shi ne ko shakka babu ya gagari al’ummar karkara, irin haka ne abin ya kasance sanadiyar karancin abincin, da kuma tsadar shi a fadin Jihar ta Zamfara wanda ya yi marukar tasiri a shirye-shiryen bikin sallah karama.

 

Kimanin  kashi 65 cikin 100 suna fama da rashin abinci da tsadarsa, wannan ko shakka babu su ne za su kawo ma shagalin sallah cikas,sabo da yadda suka kasa yin noma, a gonakin su,daga karshe ma suka kaurace ma garuruwan su dan gujewa harin ‘yan bindiga da su ke kai masu babu dare naked  kuma rana.

Abin tausayi shi ne da yawa daga cikin magidanta ba su da damar sauke nauyin fidda Zakkar fidda kai, wanda addinin musulunci ya umarci kowa ne musulmi ya fidda, shi kansa da iyalansa da zarar an ga watan Shauwal. Sakamakon rashin yin noma, da kuma tsadar abinci gashi kuma babu kudi a hannun al’umma, hakan ya sa al’umma cikin mawuyacin halin da suke fuskanta yanzu.

Malam Umar mai awo ya bayyana ma wakilin mu cewa, tunda ya ke bai taba ganin matsalar rayuwa irin ta bana ba, ga shi dai babu isashen abinci da aka noma a wannan Jihar, kuma wanda mu ke saidawa yanzu daga wasu jiohin ake sayowa, ga tsada kuma al’ummar ba su da kudaden a hannunsu, ga dai tsadar hatsi duk da babu wani ciniki.

Yanayi da ake ciki yanzu haka masara muna sai da buhu daya Naira 20,000. Shinkafar Gumi buhu mai kyau yana kai Naira 45,000. Dawa  kuwa ita Naira 20,000 da Gero.

MOBILIZED9JA A Yau ta nemi jin ra’ayim wata mata a kan yanayin bikin wannan Sallah, Hajiya ‘Yar Tsafe ta bayyana cewa,”A matsayin mu na iyaye mata ba ta dinki muke yi ba, ta abinci da za su ci muke yi ga shi babu kudi ga kuma tsadar rayuwa” .

Shi ma Malam Mannir Taila ya bayyana wa wakilinmu cewa, “Ai sallar bana sai dai addu’a, dan ba ta dinki ake ba ga yaran mu nan kwance babu aiki, maganar abin da a al’umma za su ci ake yi, dan akwai wanda duk shekara shi ke ba mu tallafin abinci, amma a yanzu haka yau tallafin mu ya ke jira. Mu ma din abin ya kai ga ya gagara sai wane da wane, me yin kala biyar da yaran sa a bana da kyar wasu ke iyayin kala daya”.

……………………….

…Alamu Solar Nuna Da Wuya Bikin Sallah Ya Yi Armashi A Jihar Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Al’amarin Sallar Idi karama abin ya zama kwan-gaba-kwan-baya a Jihar Nasarawa sakamakon irin matsin da ake ciki.

A Jihar Nasarawa yadda Sallah za ta kasance ya sa al’ummar yin zaman zuru. Sakamakon yadda ake fama da dan karen talauci wanda ya mamaye kasar ba kawai Jihar Nasarawa ba.

Duk da cewa a ranar Littinin aka gudanar da wasan gargajiya na saniya da ake cewa ‘hawan kahon saniya’. To amma duk wannan wasan bai nuna nishadi na kusantuwar bikin Sallah kamar yadda aka saba yi ba, a shekarun baya da suka gabata.

‘Yan kasuwa solar yi zugum sakamakon babu hada-hadar jama’a, saboda rashin samun albashi na ma’aikatan kananan hukumomi.

Su ma ma’aikatan gwamnatin Jihar suna tsakiyar wata babu Kuma hada hadar harkar kasuwanci daga gare su.

‘Yan kasuwar babban kasuwa ta cikin garin Lafia suna fuskantar rashin ciniki ko kuma jama’a wadanda ke shiga kasuwar domin su sayi abubuwan da suke saidawa.

Haka nan ma ita kasuwar injin casa shinkafa da yafi gudanar da hada-hada ‘yan kasuwar, suna nan solar yi zugum duk a sakamakon babu masu saya da sayarwa.

Daga karshe kasuwan shinge da ake hada-hadan dabbobi suma babu labari  can saboda dabbobi solar yi tsada sosai. Bugu da kari kuma al”umma babu kudade a hannunsu. Ya zuwa yanzu al’ummar musulmai daga Jihar Nasarawa solar dogara da Allah, solar zura ido suna jiran ranar Sallah wadda kuma ta kasance Alhamis ce skamakon rashin ganin watan Sahuwal da ba ayi ba ranar Talata.

 

……………….

… A Kebbi Kuwa Wasu Na Murna, Wasu Na kunci

 

Daga Umar Faruk Birnin-kebbi

Al’umma a Jihar Kebbi sai murna da farin ciki suke tayi na ganin cewa lokaci gudanar da bikin karmar Sallah na shekara ta 2021 ya kama, bayan kammala azumin watan Ramadan na shekarar ban a lafiya.

 

Kan hakan ne wakilin MOBILIZED9JA AYau ya zagaya cikin garin Birnin-Kebbi don ganin irin yadda jama’a  ke shiri da kuma sayen kayan gudanar da bikin karmar Sallah, inda ya ziyarci wuraren da ake hadahadar yankan kaji da kuma kashin nama tonton don yin miyar Sallah. A wurin kashin naman tonton ya samu jin ta bakin daga daga cikin wadanda ke kashin naman a  tsohuwar mayanka Kan babbar hanyar zuwa uguwar Badariya wanda ya bukaci  a sakaye sunansa ya ce” sallar bana Alhamdulillah domin  duk abinda ya dace ga magidanci ya yiwa iyalansa kan gudanar da bikin karmar Sallah na kammala kama tun daga sayen kayan sawa har zuwa ga cefanen kayan abinci duk na hadasu. Yanzu haka da nake zantawa da kai nama ne muke  kasawa na  mutane goma da suka hada kudi har da ni muka  sawo shanu biyu akan kudi Naira dubu dari hudu da hamsi don mu yanka  sai ayi kashi kowa ya dauki nama zuwa gidansa don gudanar shagalin Sallah. Saboda hakan muna godiya ga Allah da ya hore muna abin gudanar da hidimomin sallah.”

 

Haka kuma wakilin namu ya samu zantawa da Malam Bello Ya’u da ya kawo kaji a gyara masu ya ce” na sawo kaji guda biyar akan kowace daya akan Naira dubu biyu da dari uku don gudanar da shagalin Sallah. Saboda hakan a gwargwadon hali mun shirya gudanar da shagalin Sallah batare da wata matsala ba. Bisa ga hakan sai dai mu yi fatan Allah ya sa rayuwarmu taga safiyar sallah lafiya,” in ji Malam Bello Ya’u.

 

A bangaren wasu Ma’aikatan gwamnatin Jihar ta Kebbi wadanda suka bukaci a sakaye sunayensu solar ce” da yawan ma’aikata a jihar na cike da bacin rai kan rashin biyansu kudaden hutu da kuma kudaden ritaya.  Domin duk ma’aikatan Jihar solar sa rai cewa gwamnatin jihar ta Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu za ta biya don ma’aikata su iya gudanar da shagullan sallah cikin dadin rai da kuma anna shawa, amma sai gashi hakan bai samu ba. Idan dai za’a tuna ko a ranar bikin Ma’aikata ta duniya Gwamnan Jihar ya bayyana cewa bai yi alkawarin biyan kudaden hutu da na ritaya ba a cikin jawabinsa na ranar, inji su”. Wanda tun a ranar da aka kammala taron ma’aikata basu fita dakin taron da dadin rai ba, saboda irin jawabin da gwamnan Jihar ya gabatar a ranar Ma’aikata, inji wasu  Ma’aikatan Jihar Kebbi da suka bukaci a sakaye sunayensu”.

…………………..

 

 

…karamar Sallah Ta Zo Wa Mutanen Jihar Kogi Cikin Rashin Kudi Da Hauhawan Farashi

Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

A dai lokacin da al’ummar musulmi a fadin duniya suke gudanar da bikin karamar sallah a yau, jama’a suna ta kaiwa da komawa da kuma hada hada don tunkarar bikin karamar sallar.

Wakilin Jaridar MOBILIZED9JA A Yau da ke jihar Kogi, wanda ya zazzaga tsohuwar kasuwar Lokoja, babban birnin jihar, ya ruwaito cewa kasuwar ta cika makil da masu saye da sayarwa babu masaka tsinke, sai dai kuma akasarin wadanda wakilin namu ya zanta da su solar shaida masa cewa babban matsalolin da suke fuskanta, su ne hauhawan farashin kayayyaki da kuma rashin kudi a hannun jama’a.

Wakilimmu ya zanta da wani mahauci mai sana’ar sayar da nama, mai suna Alhaji Hamisu Muhammed Lawal wanda yayi masa bayani recreation da yadda harkokin kasuwancin suke gudanar inda yace duk da cewa jama’a na fama da rashin kudade a hannunsu kuma kayayyakin solar yi tsada, amma kuma, alhamdulillah, kasuwa kam tabarkalla.

“A da muna sayar da kilo na nama akan Naira 2000, amma kuma a yanzu muna sayar da kilo akan naira N2500. Saniya ta yi tsada, sai ka dage zaka samu saniyar N300,000 ko N350,000. Yanzu wannan saniya dana yanka a yau, na saye shi N600,000, kuma  kiwon gida ne. Komai ya yi tsada, amma mun gode Allah, kasuwa tabarkallah” Inji Alhaji Hamisu Mahauci.

Har ila yau, wakilimmu ya leka layin sayar da kayayakin hatsi wadanda suka hada da shinkafa, wake, dawa, gero da kuma masara.

Mallam Muhammed Abubakar wani mai sayar da wake da shikafa ne, kuma ya shaidawa wakilimmu cewa duk da cewa babban matsalar jama’a shine rashin kudi, amma kuma kasuwa na tafiya yadda ya kamata.

“Kasuwa na tafiya kamar yadda aka saba,ba wata matsala,mu kan dauki buhun wake akan N43,000, sannan mu sayar dashi akan N46,000 ko N46,500.Haka ita ma shinkafa yar gida, muna saya akan N42,000, sannan mu sayar akan N45,000.

Duk da matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta, kasuwa dai kam Alhamdulillah” Cewar Mallam Abubakar.

Wasu daga cikin kayayakin da wakilinmu ya gano suna da dan karen tsada kuma ya zama wajibi ayi amfani da su a bikin sallar, sune Tumatir da Atarubu wadanda kayayaki ne na gwari.

Wakilimmu ya zanta da Hajiya Rukayya Yunusa, wadda seller ce a harkar na Tumatur da Atarubu,kuma ta shaidawa wakilimmu cewa a yanzu suna sayar da Tumatur akan kudi #43,000 kowani kwando, a yayin da Aturubu kuma suna sayarwa akan #30,000.

Tace karancin kayayakin da kuma kudin motar kwaso su daga inda ake nome su, suna daga cikin dalilan daya sanya farashin kayayakin suka yi sama,amma kuma acewarta, jama’a suna saya duk da cewa suna  fama da rashin kudi a hannunsu.

……………

…karamar Sallah: Muna Cikin Lokaci Na Daban Da Saura – Al’ummar Borno Da Yobe

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

A daidai lokacin da al’ummar musulmi ke gab da kammala azumin Ramadan da kankamar ruguntsumin karamar sallah, wanda bisa ga al’ada lokaci ne na hada-hada da shirye-shiryen tunkarar karamar sallah, ta fuskar tanadar sabbin tufafin kwalliya da ado na musamman ga manya da kanana, kayan abinci kala-kala domin wannan rana mai matukar muhimmanci- wadda ake yi wa lakabi da sallah bikin rana daya. Wanda hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi suna daya daga cikin abubuwan da suka bakanta fuskar shagulgulan sallar a yankin.

Wakilinmu a jihohin Borno da Yobe ya jiyo ra’ayoyin jama’a dangane da yanayin shirye-shiryen da suka yi wa sallar bana, yayin da suka bayyana cewa wannan shekara ta zo da salo na daban da sauran shekaru takwarorinta, mafi yawan jama’an nuna cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a yankin, al’amarin da ya tagayyara harkoki da walwalar jama’a, kimanin shekaru 11 da suka gabata, wanda a halin da ake ciki dubun-dubatar jama’ar suna ci gaba da rayuwa a matsugunan yan gudun hijira a cikin Nijeriya da wasu kasashen makobta.

Malam Madugana Maiduguri a jihar ya bayyana cewa, “gaskiya a zahiri babu alamar karsashi a wannan sallah kamar yadda aka saba a shekarun baya, saboda idan ka duba babu kudi a hannun mutane, sannan ga irin yadda kayan abinci da masarufi suke tashin gwauron zabi a kowace rana. Kuma hakan ya biyo bayan dogon lokacin da wannan yanki ya dauka yana fuskantar kalubalen tsaron rikicin Boko Haram, wanda ya tagayyara rayuwar jama’a da abinci zaka ji ko hidimar sallah?”

A nashi ra’ayin, Alhaji Abubakar Usman, mazaunin birnin Damaturu a jihar Yobe ya bayyana cewa, “to, karamar sallah bana ta zo mana daban da sauran lokuta makamantanta, ta riski mutane a wannan jihar cikin mawuyacin matsin tattalin arziki wanda ya zo sakamakon rikicin Boko Haram, wanda idan ka kalli mutane zaka ga babu alamar shaukin cewa muna tunkarar bukukuwan sallah, hana rantsuwa nama da dan abinda ba a rasa ba na tanadin abincin sallah, amma sauran sai abinda hali ya yi.”

Haka zalika, idan mutum ya ziyarci wuraren da aka saba gudanar da hada-hada da ruguntsumin sallar, irin su wuraren teloli, shagunan sayar da yaduka da atamfofi da leshin mata da makamantansu, suma zancen daya ne, babu cincirindon jama’a kamar yadda aka saba a wadannan jihohin, duk da ana samun jama’a nan da can, amma ba kamar sauran shekaru ba.

…………………

Yanayin Da karamar Sallah Ta Zo Wa Al’ummar Jihar Jigawa A Bana

 

Daga Munkaila Abdullah, Dutse

A jihar Jigawa kamar yadda aka sani jiha ce wadda fiye da kaso casa’in cikin dari na al’ummarta suka kasance musulmai dan haka suma duk da irin yanayin kalubalan na rayuwa bai sa solar fasa shirye-shiryen yadda za su gudanar da Sallah karama ba.

Haka kuma jihar na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma wadanda sukayi dacen samun zaman lafiya akan sauran jihohin dake makwabtaka dasu.

Wannan yanayin zaman lafiya ya sanya gwamnatin sahalewa Al’ummar jihar dasu gudanar da shagulgulan bikin sallah Kamar yadda aka saba tareda kiyaye dukkanin matakan kariya daga cutar nan ta korona.

Sannan duk da wannan yanayi na zaman lafiya, Kakakin rundunar ‘yansanda reshen jihar SP Zubairu Aminuddeen Ismail ya ce rundunar tasu ta baza ‘Yansanda samada dubu hudu a kannan hukumomi 27 dake fadin jihar domin tabbatarda anyi sallah lafiya.

Dangane da yanayin tattalin arziki kuwa, management ayau ta kewaya lungu da sakunan jihar domin jin ra’ayoyin Al’umma kan shirye-shiryen bikin sallar kuma solar shaida mana cewa sallar ta bana sai dai addua kawai.

Malam Mukhatar Sani wadda keda yara shida da mata daya, yace a wannan shekara iyalan nasa babu wadda zai sami kayan sallah Ballantana maganar naman sallah.

Shi kuwa wani mai suna Usman Mohd cewa yayi duk tinaninsa bai wuce ya za’a samu abinda za’a ci ba, bawai maganar kaya ko naman sallah ba.

Malam Adamu Lawan, wani mai sayarda shinkafa ne a Birnin Dutse kuma ya shaida mana cewa duk da cewa a bara akwai dokar takaita zirga-zirga amma anfi samun kasuwa fiye da wannan shekara.

Yace a bana babu hada-hadar kasuwa Kamar shekarar information gabata wadda acewarsa wannan nada alaka ne da matsin tattalin arzikin da Al’umma suka tsinci kansu a ciki.

Malam Adamu ya kuma ce, farashin mudun shinkafar tuwo a wannan shekara bai haura naira 1,300 ba yadda a waccan shekarar kuwa ya haura wannan farashin.

Shi ma Malam Abubakar Jibril Tela cewa yayi, duk da kasancewar Akwai dokar hana zirga zirga a shekarar information gabata amma, sunfi samun aikin dinkunan sallah akan wannan shekara.

Dangane da kayan miya kuwa, Management ayau ta tattauna da malam Ismail mai kayan miya, yace shekarar bara tafi hada hada akan wannan shekara.

Yace a wannan shekara mudun tattasai ya kai naira 900, kwandon tumatur naira dubu 20 wadda a cewarsa tsadar abubuwa suka hana Al’umma hidundumun sallah a wannan shekara.

Shi kuwa malam Jafar Shehu mai gyaran kaji, cewa yayi babu ko shakka wannan shekara babu kasuwa Kamar shekarar da ta gabata, ya kuma alakanta hakan da sanarwar dake zagaya wa kan cewa babu tabbacin rana daya da za’ayi sallah (Laraba ko Alhamis ) yadda yace kowa na tsoro babu tabaci rana guda.

 

 

- Advertisement -