Yadda Jirgin Kasa Ya Yi Hadari A Kaduna

0
83

Yadda Jirgin Kasa Ya Yi Hadari A Kaduna

Daga Mustapha Abdullahi,

Sakamakon matsalar sace madaurai da Takalman da ke rike da karafun titin Jirgin kasa a daidai Unguwar Kanawa cikin garin Kaduna ya haifar da watsewar Taragon Jirgi guda hudu daga cikin sha biyar na kayan bututun ruwa da Jirgin ya dauko daga Tashar Jirgin ruwan Apapa Legas zuwa Saye a birnin Zariya.

Kamar yadda shugaban shiyya na tashar Jirgin kasa, Yarima Isma’il Adebiyi ya shaida wa manema labarai a wurin da hadarin ya faru, cewa wannan shi ne sawu na biyar da suka dauko na kayan bututun ruwan da suke kaiwa Saye a Zariya cikin Jihar Kaduna.

Isma’il ya ce daman can akwai tsarin da ake da shi na za a yi wa dukkan wuraren da ake daura kusoshin da ke daure titin Jirgin Kankare da nufin yin maganin masu sace kayan titin Jirgin.

Daga nan ya yi kira, “Muna kira ga iyaye da daukacin jama’a da su yi wa ‘ya’yansu magana su ja masu kunne a kan irin yadda suke kokarin lalata titin jirgi, kamar yadda wannan hadari ya faru a cikin garin Kaduna ne kuma duk ya faru ne sakamakon matsalar sace-sacen kayan titin Jirgin da wasu ke sacewa su kaiwa wani mutum a can wani wuri a sayar masa a kudi kadan”.

Ya kara da cewa mutanen Arewa su na da kokarin yin amfani da Jirgin kasa ta fuskar daukar mutane.

Wakilinmu da ya shaida mana cewa taragon jirgin da suka yi hadarin, duk solar watsar da kayan bututun da suka dauko, amma babu labarin asarar rayuka ko jin rauni.

What's On Your Mind?