Yadda Idin Karamar Sallar Ya Gudana A Daura

- Advertisement -

Yadda Idin Karamar Sallar Ya Gudana A Daura

Daga Sagir Abubakar Katsina,

Rahotanni daga Daura solar bayyana cewa daruruwan al’ummar musulmi ne suka halarci sallar idi ta wannan shekarar a filin idi na babban birnin Daura.

Wakilinmu ya ruwaito cewa filayen idi guda biyu solar samu halartar musulmi wadanda suka sanya sabbin tufafi.

Haka nan kuma an tura jami’an tsaro a masallatan guda biyu da sauran muhimman wuraredomin sanya idodon gudanar da sallaracikin kwanciyar hankali.

Babban limamin masallacin juma’a na gidaje masu saukin kudi da e Daura Sheikh Musa Mansir, Adam shi ne ya jagoranci sallar raka’a biyu da ta gudana a farfajiyar makarantar firamare ta Mallamawa da ke Daura.

A hudubar da ya gabatar Sheikh Musa Mansir Adam ya yi kira ga al’ummar musulmi da su tsarkake zuciyarsu domin cigaban al’umma.

Sheikh Musa Mansir Adam ya tunansar da al’umma da su gudanar da azumi na Sitta Shawwal a wannan wata da muke ciki na Shawwal.

Malamin Addinin musuluncin ya kuma bukaci al’ummar musulmi das u cigaba da gudanar da ayyuka masu kyau har bayan azumin watan Ramadan, sannan kuma sai yayi addu’ar Allah (SWT) ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiha da kuma kasa baki daya.

Bayan kammala sallar dai al’ummar Daura ta kai gaisuwar Sallah ga mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk domin neman albarkarsa da kuma yi masa addu’o’i da gaisuwar barka da Sallah.

Masarautar dai ta soke hawan karamar Sallah saboda yanayin tsaro da ake fama da shi a Jihar Katsina.

- Advertisement -