Yadda Aka Yi Jana’izar Mahaifiyar Sarakunan Kano Da Bichi

0
130

Yadda Aka Yi Jana’izar Mahaifiyar Sarakunan Kano Da Bichi

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da tawagar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Alhaji Ibrahim Gambari tare da Ministocin tsaro, shari’a, zirga-zirgar jiragen sama da albarkatun ruwa na daga cikin dubban al’ummar Musulmi da suka halarci jana’izar mahaifiyar sarakunan Kano da Bichi, Hajiya Maryam Mai Babban daki.
Har ila yau Mai Alfarma Sarkin Musulmi Wanda Wazirin Sokoto ya wakilta, da sarakunan Hadejia, Nungi, Kazaure, Abaji, Matawallen Borno da sauran sarakuna da manyan baki suna cikin wadanda suka yi mata sallah bayan solar tarbi gawarta a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano yayin da aka dawo da ita daga kasar Masar ta Abuja.
An iso da gawarce ‘yan mintuna kadan kafin karfe shida na yammacin ranar litinin.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauran iyalai ne suka rako gawar mamaciyar zuwa Kano. Dubun dubatar mutane ne suka hallara  a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano suka shaida isowar marigayiyar.  Yayinda hanyoyi da yawa suka kasance a cunkushe da al’umma tun daga filin jirgin har zuwa Fadar Sarkin Kano.

Kafin tafiya filin sauka da tashin jiragen saman na Malam Aminu Kano, tawagar Gwamnatin tarayya ta kasance a fadar Sarkin na Kano tare da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da saura sarakuna inda suka isar da sakon ta’azziya ga Masarauta da al’ummar Jihar Kano.

Farfesa Gambari ya yaba da rayuwar marigayiyar, Hajiya Maryam Ado Bayero (Mai Babban daki) inda ya ce jinin sarauta na kwarara zuwa dangin kowane bangare na iyaye. “Alhamdulillah ita ce Mahaifiyar Sarakunan Kano da Bichi.”

Bayan kammala takaitaccen jawabinsa sai ya mika abin magana ga Ministan harkokin jiragen sama Sanata Hadi Sirika, wanda ya yi addu’ar fatan Allah ya kyautata makwancinta.

Da yake gabatar da jawabinsa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jinjinawa Gwamnatin tarayya da Jihar Kano bisa kulawa da kuma damuwar da suka nuna Mana, ya bayyana marigayiyar da cewa, “uwace ga kowa. Ba ma daukarta a matsayin Mahaifiyar mu kadai, uwace ga kowa.  Haka ta nuna mana alokacin tana raye.”

“Amadadin masarautar Kano da Bichi, da sauran Masarautun Jihar Kano, Gwamnati da al’ummar Jihar Kano muna matukar godiya bisa wannan muhimmiyar ta’azziya.” In ji shi.

Daga nan aka dunguma zuwa kofar kudu dake Fadar Sarkin na Kano, inda babban limamin Kano Farfesa Muhammad Sani Zaharaddin ya jagorancin sallatar gawar mamaciyar, ‘yan mintuna kafin karfe bakwai aka kwantar da ita a makwancinta a hubbaren dake cikin Gidan Sarkin Kano.

What's On Your Mind?