Yadda Aka Yi Bikin Nadin Sheriff Kamilu A Matsayin Sabon Turakin Lokoja

- Advertisement -

Yadda Aka Yi Bikin Nadin Sheriff Kamilu A Matsayin Sabon Turakin Lokoja

Daga Ahmed Muh’d Danasabe,

Ranan Asabar, 15 ga watan Mayu,2021, rana ce da Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina da iyalansa da ‘yan uwa da kuma abokanansa na arziki, ba zasu taba mantawa a rayuwarsu ba, domin kuwa a wannan rana ce, mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi Na 111, OON, ya nada Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina a matsayin sabon Turakin Lokoja, a fadarsa.
Bikin wadda ya samu halartan jama’a daga sassa daban daban na jihar Kogi da kuma wajen jihar,, yayi armashi matuka gaya.
Fadar Sarkin na Lokoja, ya cika makil da jama’a babu masaka tsinke,duk da ruwan saman da aka dinga tafkawa kamar da bakin kwarya.
Da yake jawabi kafin nadin sabon Turakin, mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi Na 111, yace ya nada Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina a matsayin sabon Turakin Lokoja ne  duba da irin dimbin gudunmawar da mahaifinsa, marigayi Sheriff Kawu Zangina ya bayar wajen ci gaban Lokoja a yayin da yake raye.
Sarkin ya bayyana cewa sau da dama mahaifinsa yana bayyana gaban kotu domin kare kima, martaba da kuma mutuncin masarautar Lokoja a lokacin rayuwarsa shekaru da dama da suka shude, wannan dalili, a cewar sarkin ya kamata a saka masa ta baiwa dansa Turakin Lokoja, duk da cewa shi Sheriff Kawu Zangina baya raye, inda ya kara da cewa alheri danko baya faduwa kasa banza.

Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi, wanda yace duk da cewa shi kansa sabon Turakin yana bada gagarumin gudunmawarsa wajen ci gaban masarautar Lokoja, duk da hakan irin dimbin gudunmawar da mahaifinsa ya bayar wajen kare mutunci da martaban masarautar Lokoja, basu misaltuwa.
Alhaji Kabir Maikarfi har ila yau yayi kira ga Alhaji Sheriff Kamilu daya tabbatar ya hada kai da mai unguwar gundumar Ward D, wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin daya fito tare da kwatanta adalci ba tare nuna son kai ko son zuciya ba,
Kazalika ya shawarci sabon Turakin daya rika hakuri da jama’a ganin cewa a yanzu nauyi na kansa.
Sarkin na Lokoja ya kuma yi nuni  da cewa sarautar Lokoja bana sayarwa bane, amma kuma ana bada shine ga wadanda suka kawo ci gaba ga garin Lokoja, koda kuwa talaka ne.
Mai martaba Sarkin na Lokoja haka nan kuma ya tabbatarwa da sabon Turakin na Lokoja, Alhaji Sheriff Kamilu cewa daga ranan nadinsa a Matsayin Turaki, ya zama yana daya daga cikin masu rawanin sarki, sannan yayi kira gare shi daya baiwa marada kunya.
Daga nan Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi ya taya sabon Turakin na Lokoja, Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina murnan nada shi da kuma kasancewa  sabon Turakin Lokoja.
A jawabinsa kadan bayan yi masa wakan sarauta, sabon Turakin na Lokoja, Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina, ya godewa mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi na 111, a bisa nada shi a Matsayin Turakin Lokoja, inda har ma ya jaddada godiyarsa da kuma farin cikinsa bisa ganin wannan rana mai albarka.
Yace babu abiinda zai cewa sarki, sai godiya.
Alhaji Sheriff Kamilu Zangina har wa yau ya bayyana godiyarsa ga sauran jama’a musamman masu rike da rawanin sarki  da abokanan arziki da kuma yan uwa wajen ganin an samu gagarumin nasara a yayin nadinsa a Matsayin Turakin Lokoja.
Ya kuma tabbatarwa da Sarkin Lokoja da sauran jama’a cewa, da yardan Allah zai baiwa marada kunya.
Bayan kammala nadin sabon Turakin ne, sai yan uwa da abokan arziki da sauran jama’an gari suka raka sabon Turakin na Lokoja zuwa gidansa dake unguwar Madabo a birnin Lokoja, inda makada da mawaka, musamman masu busa algaita suka baje kolinsu domin taya sabon Turakin na Lokoja, Alhaji Sheriff Kamilu Kawu Zangina murnan kasancewa sabon Turakin Lokoja.
An dai yi biki lafiya,kuma an kammala lafiya.

- Advertisement -