Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

0
9

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Garba Ibrahim Shekara, ya tabbatar da yadda suka yi watsi da wasu ’yan takara guda shida, wadanda suka gaza tsallake gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda ya bayyana cewa, jamiyyun da ’yan takarar suka fito na iya maye gurbinsu cikin satin nan da ake ciki.

Gabanin zaben 16 ga Janairu, 2021, na kananan hukumomin Jihar Kano guda 44, hukumar KANSIEC tun a ranar Laraba ta ce, ta yi watsi da wasu ’yan takara guda shida, saboda photo voltaic kasa tsallake gwajin kwayoyin da aka gudanar a kansu.

A yayin da yake karin haske kan batun, Farfesa Sheka ya ce, Hukumar zaben ta KANSIEC ta kirkiri gwajin kwayoyi ne a matsayin wajibi ga duk dan takarar da ke son neman kujerar shugaban karamar hukuma ko kansila a zabe mai zuwa, saboda yawaitar shaye-shaye da ta’amalli da miyagun kwayoyi a jihar ta Kano.

Dalilan Da Suka Sa Maza Suka Fi Mata Saurin Mutuwa

Ya ce, “bayan gwajin kwayoyin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gudanar ga duk ’yan takarar ciyamomi 44 da kansiloli 484, an tabbatar da shida daga ciki ’yan kwaya ne kuma mun cire su daga jerin ’yan takara.

“Dukkan ’yan takarar guda shida masu zawarcin kujerar kansila ne, babu dan takarar shugabancin karamar hukuma. Jamiyyunsu na iya amfani da wannan satin, don gabatar da wasu ’yan takara,’ inji shi, ya na mai cewa, dokar zata zama izna ga matasa masu sha’awar siyasa da su guji shaye shaye.

What's On Your Mind?