Yadda Aka Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iyayensu

- Advertisement -

Yadda Aka Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iyayensu

Daga Mustapha Abdullahi, Kaduna

A cikin makon nan ne cikin hukuncin Allah daliban makarantar Koyar da aikin Gona da al’amuran Gandun daji da ke Kaduna suka samu kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace su a wani dare cikin harabar makarantar da ke Unguwar Afaka ta karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

daliban na cikin murnar sake haduwa da iyaye da ‘yan uwa tun bayan da aka sace su a cikin makarantar inda suka kwashe tsawon kusan watanni biyu a hannun ‘yan bindiga a cikin daji.

daliban dai solar yi bayanin cewa tsawon zamansu a wurin ‘yan bindigar ana ba su Tuwo miyar kuka ne sau daya a rana inda suka tabbatar wa manema labarai cewa babu dai maganar ingantaccen abinci ko kadan.

Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan mika daliban ga iyayensu ‘yan uwa da abokan arziki, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan, bayyana godiyarsa ya yi da nasarar kubutar da daliban, inda ya kara tabbatar wa da jama’a cewa Gwamnati na iyakar bakin kokarinta domin kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da sauran makamantansu.

Shi kuwa Kwamishinan ,yan Sanda na Jihar Kaduna Umar Muri cewa ya yi suna nan su na kokarin kubutar da daliban jami’ar Greenfield mai zaman kanta da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kuma ya ce za a samu nasarar da ake bukata in Allah ya amince.

Shi ma Shugaban makarantar koyon aikin Gona da Gandun dajin’ Dokta Bello Mohammed Usman cewa ya yi suna murna da farin cikin sake hada dalibai da iyayensu kuma nan gaba kadan za a ci gaba da gudanar da aiki kamar yadda aka saba a cikin makarantar.

“Nan gaba kadan dalibai za su rubuta jarabawarsu saboda daman solar kusa fara jarabawa ne wannan al’amari ya faru”, in ji shi.

A wurin taron mika wa iyaye ‘ya’yansu tun bayan da ‘yan bindigar suka sace su, taron da aka yi a dakin taro na makarantar da ke Afaka ya samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki wasu na kuka, wasu kuma na rawa suna murnar sake haduwa tun tsawon kusan watanni biyu da ‘yan bindiga suka sace su.

- Advertisement -