Yadda Aka Kashe ‘Yan Sanda 16 A Nijeriya Cikin Makon Da Ya Gabata

- Advertisement -

Yadda Aka Kashe ‘Yan Sanda 16 A Nijeriya Cikin Makon Da Ya Gabata

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

 

An ci gaba da kai hare-hare a kan jami’an tsaro musamman na ‘yan sanda a wasu sassan Nijeriya a makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar akalla jami’ai 16.

 

Binciken da MOBILIZED9JA A Yau ta yi bisa nazarin rahotannin jaridu da bayanan da jami’an gwamnati suka bayar a hukumance ya nuna cewe, an kashe jami’an 16 ne a wasu hare-hare da aka kai ofisoshin ‘yan sanda hudu daban-daban a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin Nijeriya. Yankunan biyu a cikin ‘yan makonnin da suka gabata solar fuskanci hare-hare da ake kai wa jami’an tsaro da cibiyoyi.

 

Idan ba a manta ba, jaridarmu ta ruwaito yadda aka kashe ‘yan sanda 18 a wasu hare-hare daban-daban a fadin Nijeriya a makon da ya gabata.

 

Kashe-kashe da lalata ofisoshin ‘yan sanda solar fara kamari ne kimanin wata guda da ya gabata, kuma tun daga wannan lokacin ya ci gaba duk da kame da kashe wasu da ake zargi da lamarin.

 

An zargi kungiyar IPOB, haramtacciyar kungiyar nan ta ‘yan awaren biyafara da reshenta na daukar makamai (ESN) da kai yawancin hare-haren, sai dai kungiyar ta musanta cewa tana da hannu.

 

Haka zalika, ba duka hare-haren da aka kai wa ofisoshin ‘yan sandan ba ne aka samu nasara yayin da jami’ai suka sanar da kashe wasu mutane 11 da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne yayin wani hari da suka kai kan wani kwamandan ‘yan sanda a Orlu, Jihar Imo, a ranar Alhamis.

 

MOBILIZED9JA A Yau ta yi karin haske kan rahotannin kai hare-hare a kan ofisoshin ‘yan sanda a makon da ya gabata, daga ranar 2 zuwa eight ga Mayun 2021.

 

Harin Ebonyi:

 

Akalla ‘yan sanda biyu ne aka kashe yayin da wasu da ake zargin mambobin kungiyar ta ESN ne a safiyar ranar Alhamis suka mamaye wani ofishin ‘yan sanda da ke Obiozara, karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi.

 

An ce, maharan solar mamaye ofishin da misalin karfe three na secure, kuma suka cinna wa ofishin jami’in ’yan sanda na shiyya da ke yankin wuta (DPO) da kuma ofishin gudanarwa.

 

Wannan jaridar ta samu labarin cewa an kona babban ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar yayin zanga-zangar #EndSARS, a shekarar da ta gabata.

 

Jami’an ‘yan sandan na amfani da ginin da aka kai wa harin ne a matsayin ofishinsu na wucin gadi.

 

Yadda aka Kashe jami’ai biyu a Anambra:

 

An kashe ‘yan sanda biyu yayin wani harin bindiga da aka kai a wani ofishin ‘yan sanda a jihar Anambra, Kudu maso gabashin Nijeriya, a ranar Alhamis.

 

‘Yan bindigan solar yi kaca-kaca da ofishin ‘yan sandan da ke Obosi, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar yayin harin wanda ya afku da sanyin safiyar ranar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar harin ga Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN).

 

NAN ta ruwaito cewa, maharan solar fara lalata ofishin ne kafin su afkawa gidan ‘yan sandan inda suka kashe jami’an biyu.

 

Mista Ikenga, wani mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, ya ce, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Chris Owolabi, ya tura wata tawaga domin duba yadda lamarin ya faru a kai tsaye.

 

“Tawagar dabarun karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda an umurce ta da su gudanar da aikin tantance wurin. An kuma gaya wa tawagar cewa mai yiwuwa ne su gano tare da kama maharan da suka kai harin,” in ji shi.

 

Kakakin ‘yan sandan ya ce, an ajiye gawar jami’an da aka kashe a dakin ijiye gawa na kusa da su.

 

Ya ce, ‘yan sanda solar fara bincike kan harin.

 

Gazawar Harin Imo:

 

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ta ESN ne a ranar Alhamis solar kai hari a ofishin ‘yan sanda a jihar Imo. Sai dai, an fatattaki maharan kuma an kashe 11 daga cikinsu, a cewar wani jami’in hukumar.

 

Mai magana da yawun rundunar, Mohammed Yerima, ya ce, ‘yan bindigan solar kai harin ne kan kwamandan yankin da ke Orlu, Jihar Imo a daren Alhamis.

 

Jami’an ‘yan sanda da ke wajen solar fatattake da hadin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro.

 

Mista Yerima, ya ce, babu wani jami’in tsaro da aka kashe a harin yayin da aka kashe 11 daga cikin ‘yan bindigar. An kuma kwato motoci bakwai da makamai da alburusai da yawa daga hannun maharan.

 

An kashe jami’ai akalla bakwai a Ribas:

 

An kashe jami’an ‘yan sanda bakwai a wasu hare-hare da dama da aka kai a daren Juma’a a Jihar Ribas, Kudu maso kudancin Nijeriya.

 

‘Yan sanda a jihar solar tabbatar da kai harin kuma solar bayar da rahoton cewa, an kashe jami’an ‘yan sanda uku a ofishin ‘yan sanda na Elimgbu, yayin da aka kashe wasu biyu a hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Rumuji.

 

An kashe wasu jami’ai biyu a wani hari da aka kai a shingen binciken jami’an tsaro a kan hanyar gabas zuwa yamma.

 

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya ce, zai yi wa ‘yan jarida cikakken bayani kan hare-haren bayan ziyarar da suka kai wurin.

 

An kashe jami’ai shida a Akwa-Ibom:

 

‘Yan sa’o’i kadan bayan harin na Ribas, wasu mutane dauke da makamai solar kai irin wannan harin a wani ofishin ‘yan sanda da ke makwabtaka da jihar Akwa Ibom.

 

An ce an kashe ‘yan sanda shida a harin na Akwa Ibom wanda ya afku da sanyin safiyar Asabar a wani ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Ini ta jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Odiko MacDon, ya tabbatar wa menema labarai da harin, da yammacin Asabar.

 

Ya ce, ‘yan bindigar solar lalata wani bangare na ofishin ‘yan sandan.

 

“’yan bindigar solar je barikin ‘yan sanda inda jami’an ‘yan sanda ke barci suka harbe su har lahira,” in ji wani jami’in gwamnatin jihar.

 

Cewar wani Masanin harkokin tsaro:

 

Wani masanin harkokin tsaro kuma tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Sani Usman, yayin da yake tsokaci kan hare-haren ya bukaci gwamnatoci da su magance matsalar tun kafin ta yi yawa.

 

Birgediya Janar din mai ritaya ya kara da cewa, hare-haren ba alheri ba ne ga tsaron kasar.

 

“Ba shi da kyau ga zaman lafiya da tsaron wannan al’ummar. Saboda haka, akwai matukar bukatar bullowa da aiwatar da dabarun dakile ta tun kafin abin ya wuce gona da iri,” in ji shi.

 

- Advertisement -