Yadda Aka Kama Hatsabibin Barawon Da Ya Saci Wayar Hannu 273 A Katsina

- Advertisement -

Yadda Aka Kama Hatsabibin Barawon Da Ya Saci Wayar Hannu 273 A Katsina

Daga Sagir Abubukar, Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinanta, Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar cafke wani kasurgumin barawo da ya kware wajen balle gidaje ya yi sata da kuma satar mashina, mai suna Abba Kala dan shekara 23 da haihuwa da ke zaune a Unguwar Fegi, a karamar hukumar Daura ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce An kama shi ya je yin sata gidan wani Kamilu Ibrahim da ke da shekara 33 yana zaune a Unguwar Shagari cikin garin Daura, inda wanda ake zargin ya fasa gilassan Motar Kamilu kirar BMW three Collection mai lamba JW 01 DRA, Inda ya saci wayoyin hannu kwara dari biyu da saba’in da ukku, Wanda an yi kiyasin kudin su naira Miliyan goma sha biyar.

A cikin binciken da yan sanda suka yi an samu jimlar wadannan wayoyin hannu guda 273 a hannun sa ba tare da bacewar ko saida ko guda ba. Kuma tuni ya amsa laifinsa da zaran an gama bincikensa za’a maka sa gaban kuliya manta sabo, kamar yadda SP Gambo Isa ya tabbatar wa manema labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina.

- Advertisement -