Yadda Aka Cafke Mutum Biyu Da Kokunan Kawunan Mutane A Makabartar Kaduna

0
165

Yadda Aka Cafke Mutum Biyu Da Kokunan Kawunan Mutane A Makabartar Kaduna

Daga Mahdi M. Muhammad da Abubar Abba, Kaduna

A ranar Asabar, Rundunar ‘Yan Sanda reshen Jihar Kaduna ta tabbatar da kame wasu mutane biyu da ake zargin matsafa ne da kokunan kawunan mutane a makabartar Musulmi.
ASP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce, an kama wadanda ake zargin da fartanya na hakar kabari.
A cewarsa, “A ranar 23 ga Afrilu, 2021, da misalin karfe 9:30 na dare rundunar ta samu kiran waya cewa wasu mutane da ake zargi da aikata wani danyen aiki an gansu a makabartar Musulmi da ke Kudenden.”
Jalige ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da, Abdulaziz Jimoh mai shekaru 68, na Zaki Shut, Kabala West Kaduna, da Mohammed Isa, 30 na adireshi iri daya.
“Da samun rahoton, ba tare da bata lokaci ba aka tura jami’an tsaro zuwa yankin inda suka yi nasarar cafke wadanda ake zargin. Abin da aka samu daga mutanen su ne, fartanya da wasu kashin mutane,” in ji shi.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

What's On Your Mind?