Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Sallar Idi A Kaduna

- Advertisement -

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Sallar Idi A Kaduna

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya jagoranci sauran ‘yan Ahlul Faidhaiti Mai Diwani Group wajen gabatar da sallar idil fidir ta bana a Kaduna a ranar Alhamis da ta gabata.

Sallar idin wadda ta gudana da misalin karfe takwas na secure a harabar Zawiyyar Ahlul Faidhati da ke Sabon Garin Tudun Wada Kaduna, ta samu halartar mutane daban-daban daga ciki da wajen Kaduna.

Da yake gabatar da huduba bayan kammala sallar mai raka’a biyu, Shehu Isma’ila Almaddah ya bayyana godiya ga Allah a kan falala da rahamar ya yi wa Al’ummar Annabi Muhamamdu (SAW).

Ya kara da cewa, “Mun gode da muka ga Ramadan na shekarar 1442/2021. Allah ya karba mana, Allah ya karba wa dukkan Musulmi.”

Dangane da darussan azumin na Ramadan kuwa, Almaddah ya ce babban darasin da ya kamata kowane Musulmi ya yi la’akari da shi a cikin Ramadan kuma ya yi aiki da shi a cikin Ramadan da wajensa shi ne tsoron Allah, yana mai cewa, “Darussan da muka dauka a ciki, dama a Allah ya ce an wajabta mana Ramadan saboda mu yi takawa (tsoron Allah). Azumi na farilla na rashin ci da sha da saduwar iyali na bana ya kare, sai dai nafila. Daga cikin wannan nafila akwai guda shida da ake yi a wannan watan na sallah na Shawwal. Kuma Annabi (SAW) ya ce wanda ya yi Ramadan ya biya da shida na Shawwal kamar ya yi azumin zamani ne duk gabadaya.”

Har ila yau Shehu Isma’ila ya bukaci al’ummar musulmi su ci gaba da aiki na kamewa daga barin abubuwan da ba su dace ba bisa tsoron Allah da yanayin matakansa kamar yadda yake a matakai na Musulunci da Imani da Ihsani, inda ya ce, “ Azumi da ake kira da “Siyamu” na rashin ci da sha da saduwa da iyali daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana ya kare amma azumin da ake kira da “Saumu” yana nan, kullum a ciki muke. Shi ne mu kame daga barin abubuwan da ba su dace ba a kowane mataki na Musulunci.”

Ya ba da misali da Sayyida Maryam mahaifiyar Annabi Isah (AS) wacce ta ci dabino ta sha ruwa lokacin da ta haifi Annabi Isah amma sai ta dauki azumi na Saumu, ma’ana ta ce ta kame, ba za ta yi magana da kowa ba da sunan bayar da amsa a kan yaron da ke tare da ita. “To wannan shi ake ce wa Saumu, kamewa.” Ya bayyana.

Wakazalika Shehu Isma’ila ya bayyana cewa Manzon Allah (SAW) yakan ci dabino kafin ya fito sallar Idil fidir, don haka kowa ya rika yin koyi.

Haka nan ya tabo batun fitar da Zakkar Fidda kai wanda ya ce ta wajaba a kan kowane magidanci ya fitar wa wanda ciyar da su ta lazimta a kansa.

Haka nan ya kwadaitar da al’ummar musulmi sport da muhimmancin yin ado da sa turare a lokacin bikin sallah.

Bugu da kari ya tunatar sport da yin Zikiri mai yawa a lokacin na sallah domin godiya ga Allah da kuma samun ambaton Ubangiji a kan bayinsa, yana mai cewa “Allah ya ce ku ambace ni zan ambace ku. Sannan mu dage da yin Salati ga Manzon Allah (SAW) domin mu nuna godiya da Allah ya ba mu shi (SAW).”

Shehu Isma’ila ya kuma jinjina wa Sahabbai bisa gudunmawar da suka bayar ga Musulunci tare da yi musu addu’ar Allah ya kara musu daraja a wurinsa.

Shehu Isma’ila ya yi addu’o’i na dan wani tsawon lokaci ga Jihar Kaduna da Nijeriya da dukkan kasashen musulmi a kan Allah ya yaye musu dukkan abin da ya dame su da kuma samun zaman lafiya mai dorewa da karuwar arziki.

Haka nan ya yi wa Falasdinawa addu’a ta musamman a kan Allah ya taimake su, sannan Allah ya karya Isra’ila tare da Amurka da ke mara mata baya a kan zaluncin da take yi a yankin Falasdinawa.

- Advertisement -