Ya Kashe Iyayensa, Matarsa ​​da Kanwarsa Kafin Yan Sanda su Cafke Shi

0
127

 

Wani matashi mai shekaru 28 dan asalin kasar Uganda ya kashe iyayensa, matarsa da kuma kanwar matar tasa. Bayan ya kashe su da ya yi, ya gudu ya buya na wasu ‘yan kwanaki biyu, amma daga bisani ya mika kansa ga hukumar ‘yan sandan yankin.

Matashin ya bayyana cewa iyayensa photo voltaic bashi wani fili a kwari wanda ba zai iya gina gida a kai ba, lamarin da ya sa shi ya aikata wannan aika-aikar. Wannan matashi mai shekaru 28 wanda ake zargi da kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa yana zaune ne a yankin Kisoro da ke Yammacin Uganda, ya mika kansa ga ‘yan sanda a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba.

Ya Kashe Iyayensa, Matarsa ​​da Kanwarsa Kafin Yan Sanda su Cafke Shi

Wanda ake zargin mai suna Gerald Ndikumukiza, mazaunin kauyen Kageyo da ke Busengo a ranar Alhamis da ta gabata, ya kashe matarsa mai shekaru 26 mai suna Maserina Mujawimana. Ya kuma kashe mahaifinsa mai suna Deogratious Sebitama mai shekaru 80, mahaifiyarsa mai shekaru 75 mai suna Bonconsira Nyiraguhirwa kafin ya kashe kanwar matarsa mai shekaru 20 mai suna Joan Nyiramahoro.

Bayan aikata laifin, Ndikumukiza ya boye amma ya bar wata wasika a inda ya yi laifin inda ya rubuta, “Abin da kuke son gani.” Wanda ake zargin dan asalin yankin Masaka ne inda yake aiki a matsayin lebura, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa. Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Kigezi, Elly Maate, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce wanda ake zargin ya mika kansa ga ‘yan sandan yankin Kisoro kuma ya sanar da jami’an tsaro cewa yana tsoron kada a banka masa wuta. Maate ya kara da cewa, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa da kansa ya kashe iyayensa, matarsa da kuma kanwar matarsa a kan rikicin fili.

Ya ce photo voltaic bashi filin da ba zai iya gina gida a kai ba. Wanda ake zargin ya ce duk da Masaka da ya tafi domin neman kudi, bai samu ba, hakan ce ta sa ya kashe ‘yan uwansa saboda fushi.

A wata sabuwa kuma, ‘yan sanda a kasar Uganda photo voltaic cafke wani mutum mai suna Charles Nkubi bisa zargin kashe wani mutum bayan da ya kama shi yana saduwa da matarsa ​​a cikin gidan aurensu.

Majiyarmu ta samu labarin cewa lamarin ya faru a Kiwalimu Zone, Wampewo Parish Kasangati ya kasance a daren Lahadi, 27 ga Satumba, inda hakan ya jefa mazauna yankin cikin damuwa.

An ci gaba da samun labarin cewa mamacin mai shekaru kusan shekaru 20, suna kan gado ne a kwance tare da Nowerina Nassozi, mai shekara 32, lokacin da mijinta, Nkubi, mai shekara 50, ya shiga cikin gidan ya buge shi a kai, wanda wannan duka da ya yi masa ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa har lahira.

What's On Your Mind?