Ya Kamata Kebbi Ta Amsa Sunanta Na “Jihar Daidaito”

0
98

Ya Kamata Kebbi Ta Amsa Sunanta Na “Jihar Daidaito”

Daga Jamil Gulma Birnin Kebbi

Tun lokacin da wata kungiya ko kwamiti na wadansu dattawa da ke burin Jihar Kebbi ta karbi sunanta na jihar daidaito “Land of Ekuity” ya soma fitowa da manufofinsa a kullum sai  samun karbuwa wannan tafiyar ke yi a wajen mutane daga dukkanin sassan jihar.
Honarabul Abdullahi Muhammed Lamba (Danmasanin Yauri) shi ne kakakin wannan kungiyar kuma zanta da wakilinmu jim kadan bayan kammala zaben shugabannin a garin Argungu  inda ya bayyana cewa zaben shugabannin da aka yi yana da nasaba da soma aiki ba tare da bata lokaci ba musamman wajen tuntubar duk wanda ke da hakki ko kuma zai iya bayarda gudummawa a cikin wannan tafiyar.
Danmasanin Yauri ya cigaba da cewa
don tabbatarda jihar ta karba lakabin ta na jihar daidaito (Land of Ekuity) a maimakon irin salon mulkin da ake yi na gida daya  wannan kungiyar ko kwamitin yana neman cimma burin sa na ganin mulkin karba-karba ya sami gindin zama a Jihar Kebbi saboda ita ma ta bi sawun yan uwanta musamman wadanda ke makotaka da ita da kuma uwa-uba Nijeriya bakidaya.
Ya bayyana cewa a jihar Sakwkwato irin wannan salon mulkin ake gudanarwa inda kowa ya sani Gwamna Attahiru Bafarawa daga Sakwkwato ta gabas ya fito  bayan  kammala wa’adinsa sai Aliyu Magatakarda daga Sakwkwato ta tsakiya ya karba shi kuma bayan wa’adinsa yanzu Aminu Waziri Tambuwal daga Sakwkwato ta kudu, haka zalika a Neja da ke makotaka da Kebbi ita ma solar yi mata kashi uku da suka hada da A da B da C, Abdullahi Kure daga A ya yi gwamna sannan Babangida Aliyu daga B yanzu gwamna Sani Bello daga C. Uwa-uba haka zalika mulkin kasar nan a bisa ga wannan turbar ya ke tafiya idan aka yi la’akari da yadda ake gudanarda shi tun dawowar kasar nan a mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 inda bayan Chif Olushegun Obasanjo ya kammala shekaru takwas ya muka mulki ga Umar Musa Yar Adua, bayan Yar Adua mulkin ya sake komawa ga kudu ga shugaba Good Luck Jonathan. A kwanannan ita ma Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da wani jadawali na mukamai inda ya ke nuna bayan shugaba Buhari ya kammala mulkin sa za a tsayar da dantakarar shugabancin kasarnan daga kudu.
Mutane da dama solar yi na’am da wannan yunkurin bisa ga irin tsarin yadda aka soma wannan tafiyar bisa ga lumana ba tare da zagi ko wata barazana ba ga kowa ba illa dai tafiya ce da ke neman a yi wa yayan jihar nan adalci, wannan ya sanya manyan mutane tun kama daga yansiyasa, manyan yanboko masu aikin gwamnati da kuma wadanda suka ajiye aiki, yankasuwa da matasa daga gundumomin Kebbi ta Arewa da kudu har ma daga Kebbi ta tsakiya suke nuna sha’awar su ga wannan tafiyar tare da alwashin za su bayarda cikakkiyar gudummawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Saboda haka a matsayin mu na yayan Jihar Kebbi kuma yayan Jam’iyyar  APC masu kishin ta muna kira ga gwamna Atiku da ya zamo zakaran gwajin dafi wajen dabbaka wannan mulkin na karba-karba wanda ba shakka yin haka zai janyo masa farinjini a idon duniya sannan kuma shi ne zai tabbatarda adalcin da Jam’iyyar APC ke ikirari da shi.
Wani na hannun daman gwamna Atiku da ya nemi a sakaya sunansa kuma dan cikin garin Birnin Kebbi wanda kuma ke kallon wannan tafiyar a matsayin mataki na shimfida adalci ya bayyanawa wakilinmu da cewa duk da ya ke ba a gayyace su ba amma dai shi da sauran abokan sa da kuma dukkan magoya bayansa suna cikin wannan tafiyar kuma za su bayarda cikakkiyar gudummawa ta duk I da za su iya don ganin an canza irin salon wannan mulkin na gida daya wanda shi ne ke ruruta wutar rarrabuwar kawunan yayan jihar nan.
Wadansu majiyoyi tabbatattu daga cikin wannan kungiyar solar tabbatarwa wakilinmu da cewa wannan tafiyar ta soma da kafar dama saboda daga watanni biyu zuwa uku da soma wannan tafiyar a kullum safiya ta Allah shugabannin ta sai solar karbi kiran sababbin mambobi masu neman a saka sunayensu cikin wannan tafiyar ba tare da la’akari da bambancin Jam’iyyar siyasa ko bangare ba wanda ba shakka idan har jam’iyyar APC  mai mulki ta aiwatarda wannan to ba shakka zancen jam’iyyun adawa ya zama tarihi a Jihar Kebbi saboda wannan shi ne  burin duk wani dan kishin Jihar Kebbi.

What's On Your Mind?